Daga Mu’awuya Bala Idris, Katsina
Hukumar Samar da Hanyoyin Karkara da Bunƙasa Kasuwancin Amfanin Gona ta Jihar Katsina (RAAMP) ta gudanar da taron bita domin wayar da kan direbobi, masu amfani da hanyoyi da ɗalibai kan muhimmancin bin dokokin hanya, da nufin rage haɗurran mota da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Da yake buɗe taron, Shugaban Shirin RAAMP na Jihar Katsina, Engr. Yusuf Yahaya, ya bayyana farin cikinsa da gudanar da taron, tare da yabawa mahalarta bisa halartar da suka yi. Ya ce nasarar shirin ba za ta tabbata ba sai da haɗin kan duk masu ruwa da tsaki.
Ya bayyana cewa manufar shirin RAAMP ita ce inganta hanyoyin karkara da bunƙasa harkokin sufuri, tare da rage haɗurran mota da asarar rayuka da dukiyoyi ta hanyar ƙarfafa bin dokokin hanya. A cewarsa, taron zai ƙara wayar da kan jama’a game da muhimmancin kiyaye ƙa’idojin tuki da amfani da hanya cikin aminci.
A nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Raya Yankunan Karkara da Kyautata Ci gaban Al’umma, Farfesa Abdulhamid Ahmad, ya yaba wa hukumar RAAMP bisa shirya wannan muhimmin taro. Ya bayyana cewa lokacin damina na ƙara haifar da ƙalubale ga masu amfani da hanyoyi, don haka akwai buƙatar ƙara wayar da kai kan matakan kariya da bin dokokin hanya.
Kwamishinan ya ce taron ya zo a kan lokaci, tare da maraba da mahalarta da suka fito daga sassa daban-daban na jihar. Ya kuma buƙace su da su yi anfani da ilimin da za su samu domin amfanin kansu da al’ummominsu.
Shi ma da yake jawabi, wakilin Shugaban Shirin RAAMP na Ƙasa, Mista Ekum Ojogu, ya yaba da haɗin gwiwar Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC), RAAMP da sauran hukumomin da suka bayar da gudummawa wajen tabbatar da nasarar taron.
A nasa gabatarwar, Jami’in Tuntuba kan Ayyukan Kiyaye Haɗurra, Engr. Okwudili N. Ikejiani, ya yi cikakken bayani kan ƙa’idojin tuki, dokokin hanya da rawar da direbobi da masu ababen hawa ke takawa wajen kare rayuka da tabbatar da tsaron masu amfani da hanyoyi.
Ya jaddada cewa bin dokokin hanya na daga cikin manyan hanyoyin rage yawaitar haɗurran mota da kuma tabbatar da lafiya da tsaron al’umma.
