Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fara tantance shirye-shiryenta na babban zaɓen 2027 a shiyyar Arewa maso Yamma.
Daga Wakilin Mu
Shugaban INEC, Farfesa Joash O. Amupitan, SAN, ya ce hukumar na ƙoƙarin gano tare da magance matsalolin da ka iya kawo cikas ga zaɓen, musamman a matakin ƙananan hukumomi da rumfunan zaɓe.
Amupitan ya yi kira ga jami’an INEC da su kasance masu tsaka-tsaki, ƙwarewa da bin ƙa’idojin aiki, yana mai cewa nasarar zaɓe tana farawa ne daga matakin ƙasa.
Ya bayyana cewa Matakai uku na Ci gaba da Rijistar Masu Zaɓe sun samar da sabbin rajista 10,772,421, waɗanda ke jiran tantancewa ta hanyar tsarin tantance bayanan halittar masu zaɓe.
Shugaban INEC ya kuma ce hukumar na aiki wajen inganta tsarin tantance masu zaɓe da aika sakamako, ciki har da sabon tsarin eEC8A.
Ya ce INEC ta ƙaddamar da tsarin wajen gudanar da harkokin kayan zaɓe, horar da jami’an wucin-gadi da haɗin gwiwa da jami’an tsaro.
Hukumar ta kuma jaddada buƙatar kawar da matsalolin rabon PVC a ƙananan hukumomi, domin tabbatar da cewa masu zaɓe da suka cancanta ba su rasa damar kaɗa ƙuri’a ba.
Taron na Kaduna na daga cikin rangadin shiyyoyi shida da INEC ke gudanarwa domin tantance shirye-shiryen jihohi da gano matsalolin da za a magance kafin babban zaɓen 2027.
