
Daga Shibili Rabi’u Sabon Titi
Gwamnatin jihar Kano za ta daga likkafar asibitin garin yan dadi da ke yankin karamar hukumar Ghari zuwa Babban asibiti
Kwamishinan Lafiya na jihar Kano Dakta Abubakar labaran shine ya tabbatar da hakan ta bakin wakilinsa
Daraktan Kula da tsaratsare da shirye shirye na maaikatar lafiya Gambo Ya’u Idris. a lokacin da ya ziyarci Asibitin garin yan dadi domin duba gyaran aiyukan asibitin
Ya kuma kara da cewa gwamnatin Enginer Abba kabir yusuf ta damu kwarai da gaske wajen kula da sha’anin harkokin Lafiya a fadin Jihar kano
A nasa jawabin shugaban karamar hukumar ta Ghari Hashim Garba Mai sabulu wanda ya samu wakilcin sakataran karamar hukumar Hashimu Sulaiman ya yabawa Gwamnatin Abba kabir bisa irin aikace aikacan da ta ke aiwatarwa a karamar hukumar Ghari na Samar musu da hanyoyi da titina da kuma daga darajar asibitin garin yan dadi zuwa babban asibitin yankin.
Shima da yake jawabinsa kansilan kula da harkokin Lafiya na yankin ya godewa gwamnana Abba kabir yusuf da ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano a karshe kuma ya jinjinawa shugaban karamar hukumar Hashim Mai sabulu yadda ya tsaya tsayin daka har aka samu wan’nan nasara.
Shibili Rabi’u Sabon Titi
Jami’in Yaɗa labarai na karamar hukumar Ghari

