GADAR KIRU TA ZAMA TARKO: Al’umma, Direbobi da ‘Yan Kasuwa Sun Koka Kan Tsayawar Aikin Hanyar Kiru–Yako
Daga Maikudi Marafa
Al’ummar Karamar Hukumar Kiru, direbobi, ‘yan kasuwa da sauran matafiya masu amfani da hanyar Kiru zuwa Yako sun bayyana damuwarsu kan yadda aikin gyaran hanyar da gada ke tafiya a hankali, lamarin da suka ce ya jefa su cikin mawuyacin hali tare da kara barazana ga rayuka da dukiyoyi.
Binciken da jaridar Fame News ta gudanar ya nuna cewa an fara aikin gyaran wannan hanya ne shekaru da suka gabata, amma har yanzu ba a kammala shi ba. A halin yanzu ma, alamu na nuna cewa aikin ya tsaya cak, abin da ya kara jefa masu amfani da hanyar cikin wahalhalu musamman a wannan lokaci na damina.
Da yake zantawa da wakilinmu, wani direba mai suna Malam ISA Danny Kiru, ya bayyana cewa rashin kyawun hanyar na haddasa matsaloli masu yawa ga direbobi da fasinjoji. Ya ce direbobi na tafiya a hankali domin kauce wa hadurra sakamakon ramuka da kwazazzabai da suka mamaye hanyar.
“Wannan hanya ta jawo mana matsaloli matuka. Muna tafiya cikin taka-tsantsan domin kare rayukanmu da na fasinjojinmu. Ramuka da lalacewar hanyar sun yi yawa, wanda hakan ke kara tsawon lokacin tafiya tare da haddasa asarar lokaci da kudi,” in ji shi.
Malam Abdullahi ya kuma bayyana cewa akwai wata muhimmiyar gada da ke kan hanyar daga Yako zuwa Kiru wadda aka rushe a yayin gudanar da aikin gyaran hanya. Sai dai tun bayan rushewar gadar, ba a kammala aikin sake gina ta ba, lamarin da ya tilasta wa direbobi komawa amfani da tsohuwar hanyar Alhazawa domin gujewa hadari.
“A sakamakon rashin kammala gadar, mun samar wa kanmu wata hanya ta daban. Yanzu mafi yawan direbobi suna bi ta tsohuwar hanyar Alhazawa saboda tsoron hatsari da kuma wahalar da ke tattare da hanyar da ake aikin gyaranta,” ya kara da cewa.
Shi ma wani dan kasuwa mai amfani da hanyar, Malam Sani Tijjani, ya bayyana cewa lalacewar hanyar na kawo cikas ga harkokin kasuwanci da kuma safarar kayayyaki. Ya ce matsalar ba wai ga direbobi kadai ta tsaya ba, har ma tana shafar rayuwar al’umma baki daya.
“Rashin kyawun hanyar Kiru zuwa Yako na jefa rayukanmu da dukiyoyinmu cikin hadari. Muna kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta dubi wannan matsala cikin gaggawa, musamman a wannan lokaci na damina da hanyoyi ke kara lalacewa,” in ji Malam Sani.
Binciken Fame News ya kuma gano cewa da zarar an yi ruwan sama, direbobi da dama na kauce wa amfani da wannan hanya saboda tsoron makalewa ko fuskantar hadurra. Hakan ya samo asali ne daga rashin kammala aikin hanyar da kuma gadar da ke hada garuruwan Kiru da Yako.
Al’ummar yankin sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ta dauki matakin gaggawa wajen sa ido da kuma tabbatar da kammala aikin hanyar Kiru–Yako da gadar da ke cikinta. Sun bayyana cewa kammala aikin zai rage wahalhalun da suke fuskanta, inganta harkokin sufuri da kasuwanci, tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
