Al’ummar Garin Dayaso Sun Koka Kan Rashin Ci Gaba, Sun Nemi Gwamnati Ta Dauki Matakin Gaggawa
Daga Maikudi Muhammad Marafa
Al’ummar Garin Dayaso da ke Mazabar Gwangwan a Karamar Hukumar Rogo, Jihar Kano, sun yi kira ga mahukunta a dukkan matakan gwamnati da su gaggauta daukar matakan magance dimbin matsalolin ci gaba da ke addabar al’ummar bayan shekaru masu yawa na rashin kulawa.
An yi wannan kira ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Makarantar Firamare ta Dayaso, wanda ya hada shugabannin al’umma, matasa, mata, manoma, mazauna garin da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna matsalolin da ke hana garin samun ci gaba.
Da yake Jawabi, Shugaban Kungiyar Raya Garin Dayaso, Malam Adda’u Usman, ya shaida wa Jami’in Yada Labarai na Karamar Hukumar Rogo cewa mahalarta taron sun cimma matsaya guda wajen gano muhimman matsaloli da ke bukatar daukin gaggawa daga gwamnati.
A cewarsa, har yanzu al’ummar garin na fama da karancin muhimman abubuwan more rayuwa, musamman wutar lantarki, duk da cewa an kafa sandunan lantarki sama da shekaru bakwai da suka gabata ba tare da hada garin da wutar lantarki ta kasa ba. Ya Kara da cewa lalacewar hanyoyi, rashin isassun magudanan ruwa da kuma karancin muhimman abubuwan more rayuwa sun yi matukar hana bunkasar tattalin arziki da walwalar al’umma.
Malam Adda’u ya kuma nuna damuwa kan halin da ilimi yake ciki a garin, inda ya bayyana cewa akwai karancin kwararrun malamai duk da cewa Dayaso ta samar da masu digiri da kwararru a fannoni daban-daban. Haka kuma ya bayyana cewa harkokin lafiya a garin na cikin mawuyacin hali, sakamakon lalacewar cibiyar lafiya da ake da ita da kuma rashin isassun cibiyoyin lafiya masu kayan aiki da za su iya biyan bukatun karuwar al’umma.
Dangane da bunkasa tattalin arziki, ya nuna damuwa kan rashin shirye-shiryen gwamnati da ke tallafawa kananan sana’o’i da manoman noman rani da damina, wadanda su ne ginshikin tattalin arzikin yankin.
Sai dai ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa amincewa da sake gina Gadar Gwangwan ta hanyar kokarin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore. Ya bayyana aikin a matsayin babban ci gaba da zai taimaka wajen inganta zirga-zirga da sadarwa a yankin.
Malam Adda’u ya kuma yi kira ga Sanatan Kano ta Kudu, Hon. Abdurrahman Kawu Sumaila; Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Mazabar Rogo, Hon. Abdullahi Sani Rogo; Shugaban Karamar Hukumar Rogo, Alhaji Abubakar Mustapha Rogo; da Kansilan Mazabar Gwangwan da su ziyarci Garin Dayaso domin ganawa kai tsaye da al’umma, fahimtar matsalolinsu da kuma nemo mafita mai dorewa.
Ya jaddada cewa al’ummar garin Dayaso al’umma ce mai sun zaman lafiya, bin doka da oda, kuma mai kishin ci gaba, wadda ke da niyyar bayar da gudunmawa mai ma’ana ga cigaban Jihar Kano da Najeriya baki daya.
A karshe, Malam Adda’u ya bukaci hukumomin da abin ya shafa da zababbun wakilai da su amsa wannan kira tare da daukar matakan da suka dace domin tabbatar da ci gaba mai anfani ga kowa da kuma inganta rayuwar al’umma.
A nasa jawabin, Hakimin Garin Dayaso, Malam Bello Alhaji Garba, ya sake tabbatar da cikakken goyon bayan al’umma ga manufofi da shirye-shiryen gwamnati karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf. Haka kuma ya yi kira ga mazauna yankin da su guji sare itatuwa ba tare da ka’ida ba, yana mai gargadin cewa lalacewar muhalli na haddasa zaizayar kasa da sauran matsalolin muhalli, ciki har da wasu daga cikin abubuwan da suka haddasa rushewar Gadar Gwangwan.
Taron ya kare da matsaya guda ta kira ga hukumomin gwamnati, zababbun wakilai da abokan hulda na ci gaba da su ba da fifiko ga ayyukan da za su inganta ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, noma da damar tattalin arziki a garin Dayaso.
