DIMOKURAƊIYYA A KAN HANYAR HALLAKA A NAJERIYA: DOMIN SANI DA ANKARAR DA YAN SIYASA DA SHUGABANNI

DIMOKURAƊIYYA A KAN HANYAR HALLAKA A NAJERIYA: DOMIN SANI DA ANKARAR DA YAN SIYASA DA SHUGABANNI

Daga Dr. Abbati Bako,psc,bsis,UK Masani a Dabarun Siyasa da Sadarwa, Tsohon Dalibin Jami’ar Kent, Burtaniya

Dimokuraɗiyya ba ta mutuwa da juyin mulki ba. Tana mutuwa ne ta hanyar zubar da jini daga raunuka dubu, kuma Najeriya na zubar da jini ta fuskar siyasa da tattalin arziƙi. Rashin tsaro ya zama labarin kullum. Abin takaici, cikin shekaru uku na gwamnatin APC, ba a sami mafita ba, musamman a Arewa. Shugaba Tinubu baicika alkawarin da yayi wa yan Najeriya.

Alamomin da ’Yan Najeriya Ke Ji Kullum

Dimokuraɗiyya na nufin “ikon jama’a.” Amma jama’a ba su da iko kan yunwa, kan masu garkuwa, ’yan bindiga, ko kan wanda zai mulke su. Talakawa ba su da iko kan hauhawar farashi, tsaro, talauci da rashin aikin yi.

Tun 1999:

1. Zaɓe ba tare da murya ba:

Muna tsayawa akan layi na sa’o’i 6 don mu zaɓa, amma kotuna ne ke yanke hukuncin wanda zai yi mulki na shekaru 4. Idan ɓangaren shari’a ya zama kwalejin zaɓe, akwatin zaɓe ya koma akwatin ba da shawara kawai.

2. Talauci da zaɓe:

Yan Najeriya miliyan 133 na cikin matsanancin talauci. Amma muna kashe Naira Biliyan 305 kan zaɓe da Naira Miliyan 160 kan Moya SUV guda ɗaya ta Sanata. Dimokuraɗiyya ba ta da tsada. Kwaɗayin shugaban nine.

3. Rashin tsaro ba tare da hukunta kowa ba wannan abin takaicine:

Yan ta’adda sun kashe ’yan Najeriya fiye da 63,000 tun 2015. Amma babu IG, Minista, ko Gwamnan da ya yi murabus. A dimokuraɗiyya, gazawa tana da sakamako. A Najeriya, tana da ƙarin girma koma matsayi.

4. Yanci ba tare da adalci ba:

An dakatar da X na watanni 7. Ana tsare yan jarida. An harbi masu zanga-zanga a Lekki. Sannan mun yi bikin “Ranar Dimokuraɗiyya.” Me muke murna da shi kenan, dimokuraɗiyya ta gaskiya ko mahaukaciyar dimokuraɗiyya?

Yadda Dimokuraɗiyya Ke Mutuwa:

Masana malamai a Jami’ar Harvard a kasar Amurka sun ce: “dimokuraɗiya tana mutuwa idan shugabannin da aka zaɓa suka lalata siyasar kuma idan babu adalci amma ba Sojoji ba. Najeriya na cika duka alamomi 4: ƙin bin ƙa’idoji, musgunawa yan adawa, yarda da tashin hankali, hana ’yancin jama’a da walwala.

Tattalin Arziƙin Hallaka:

Dimokuraɗiyya ta fi saurin mutuwa idan ciki ya koshi. IMF ta ce Najeriya na kashe kashi 96% na kuɗin shiga wajen biyan bashi. Bankin Duniya ya ce ’yan Najeriya miliyan 87 na rayuwa ƙasa da Dala 2.15 a rana. Mutum mai yunwa ba ya kare kundin tsarin mulki. Yana sayar da ƙuri’arsa kan Naira 5,000. Wannan gwanjo ne.

Zaɓen 2027 — Zaɓi Na Ƙarshe:

Zaɓuka su ne fasahar dimokuraɗiyya. Dole ne gwamnatin APC ta tabbatar da zaɓe cikin ’yanci da gaskiya a 2027. Shugaba Tinubu ya haɗiye “Umarnin Washington” 10 a kwanaki 29: tallafi ya tafi, Naira ta yi iyo, haraji ya ƙaru da kashi 240%. Idan hauhawar farashin abinci ta kasance sama da kashi 30% zuwa Disamba 2026, idan kudin Dala 1 ta kasance N1,340, idan litar fetur ta kasance ₦1,385, to zaben 2027 ba zaɓe ba ne. Zai zama ƙuri’ar raba gardama kan yunwa da talauci a Nijeriya.

Yadda Za A Farfaɗo Da Dimokuraɗiyya:

1. A ɗora sakamakon rumfuna a IReV kai tsaye. Babu ɗorawa, babu sakamako.

2. A rage kuɗin gwamnati da kashi 50%. A sayar da 70% na motocin rakiya.

3. A ɗaure babban mutum guda a gaban talabijin ya zama abin musali.

4. A biya ’yan ƙasa haqqinsu kafin a hukunta su.

5. Duk ƙararrakin zaɓe su ƙare kwanaki 90 kafin rantsarwa. Kuma aci gaba da bin Ka’idojin tsarin Demokuradiyya 57 da mash ilimi suka wanzar.

Kammalawa: Zaɓi

Najeriya na da watanni 24 don zaɓar:

Zaɓi A: Dimokuraɗiyya — inda ƙuri’u ke da tasiri.

Zaɓi B: Hallaka — inda babu zaɓuka na gaskiya wasan kwaikwayo zai zama.

Dimokuraɗiyya ba ta kai shekaru 27 ba a

Najeriya:

Ta yi shekaru 26 ana shari’ar zabe daban-daban. Hukunci zai fito a 2027. Idan muna son dimokuraɗiyya ta rayu, dole ne mu sa ta zama mai amfani. Domin babu wanda zai kare tsarin da ba ya ciyar da shi. Lokaci zai yi hukunci. Zaɓi ya rage namu ko muyi gaskiya ko muyi nadama.

Naku da aminci

Dr. Abbati Bako, Mashawarcin Dabarun Siyasa da Sadarwa kuma mai Karin yin nazari akan wani babban digiri na uku a kan tafiyar duniya bai ɗaya a Jami’ar Skyline dake Kano. Tsohon Kwamishinan Zaɓe @Kansiec, Mai Ba da Shawara na Musamman ga Tsohon Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Kuma tsohon Ma’aji a Hukumar Kasuwanci ta jihar Kano abbatibako@gmail.com

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles