Kungiyoyin Aikin Gayya a Bagwai Sun Nemi Tallafin Gaggawa Don Farfaɗo da Ayyukan Gayya
Daga Shehu Bello Shanono
Kungiyoyin aikin gayya a Karamar Hukumar Bagwai sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da kuma Karamar Hukumar Bagwai da su gaggauta samar da kayan aiki da sauran muhimman tallafi domin farfaɗo da ayyukansu, waɗanda ke da matuƙar tasiri wajen bunƙasa rayuwar al’umma a matakin ƙasa.
Shugaban Kungiyoyin Aikin Gayya na Bagwai, Malam Samaila Badau, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da Mai Ba Gwamna Shawara kan harkokin al’umma daga tushe, Alhaji Ismail Shehu Gurjiya. Ya jaddada cewa ƙarancin kayan aiki da rashin isasshen tallafi sun yi matuƙar tasiri wajen rage ingancin ayyukan kungiyoyin, duk da irin gudunmawar da suka bayar a baya wajen ci gaban al’umma.
A nasa jawabin, Mai Ba Gwamna Shawara kan harkokin al’umma daga tushe, Alhaji Ismail Shehu Gurjiya, wanda Malam Sunusi Ishak ya wakilta, ya bayyana cewa ziyarar da suka kai Bagwai na da nufin isar da muhimmin saƙo daga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf. Ya ce Gwamnan na nuna matuƙar damuwa kan raguwar ayyukan kungiyoyin aikin gayya, duk da cewa a baya su ne ginshiƙin raya al’umma a fadin jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
Ya ƙara da cewa Gwamnatin Jihar Kano na duba hanyoyin da za a bi domin farfaɗo da wadannan kungiyoyi tare da mayar da su kan sahihin tafarkin gudanar da ayyukan raya karkara yadda ya kamata.
Da yake jawabi a madadin Shugaban Karamar Hukumar Bagwai, mukaddashin Shugaban Karamar Hukumar (DPM), Alhaji Sani Umar Shanono, ya tabbatar da cewa Karamar Hukumar na da cikakken shiri na bai wa kungiyoyin aikin gayya dukkan tallafin da ya dace domin su cimma manufofinsu.
Haka kuma, ya isar da godiyar Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Bello Abdullahi Gadanya, bisa wannan ziyara, tare da yaba ƙoƙarin kungiyoyin wajen inganta rayuwar al’umma. Ya kuma jaddada aniyar Karamar Hukumar na ƙarfafa da tallafa wa duk wasu shirye-shiryen sa-kai a yankin.
Sa Hannu:
Jami’in Yada Labarai
Karamar Hukumar Bagwai
