KARAMAR HUKUMAR SUMAILA TA TAYA GWAMNAN KANO MURNAR LASHE LAMBAR GIRMAMAWA

SHUGABAN KARAMAR HUKUMAR SUMAILA YA TAYA GWAMNA ABBA KABIR YUSUF MURNAR LASHE LAMBAR GIRMAMAWA TA SHUGABANCIN KASA (NEAPS) TA 2025

Shugaban Karamar Hukumar Sumaila Alhaji Farouk Abdu Sumaila, ya taya Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf murnar lashe lambar girmamawa ta Nigeria Excellence Award in Public Service (NEAPS) 2025, wata babbar lamba ta kasa da ke girmama shugabanni masu kyakkyawan aiki da jajircewa wajen gudanar da mulki.

A sakonsa na taya murna, Alhaji Farouk Abdu Sumaila ya bayyana cewa wannan lambar yabo ba wai yabo ga Gwamna Abba Kabir Yusuf kaɗai ba bace illa sharhi ne kan irin gudummawar da gwamnatin Kano ke bayarwa wajen inganta rayuwar jama’a, tabbatar da adalci da inganta tsarin gudanar da mulki.

KARAYIN BAYANI:AN KAFA KWAMITIN KULA DA KAYAYYAKIN GWAMNATI A DAMBATTA

Ya ce lambar ta zo a lokacin da ya dace, kasancewar gwamnatin jihar ta yi fice wajen gudanar da manyan ayyukan raya kasa, kula da al’umma, da aiwatar da manufofin da suka mayar da hankali kan talakawa, musamman a bangaren ilimi, lafiya,da bawa mata jari a duk karshen wata da ababen more rayuwa da tsaro.

A wata Sanarwa da Jami’i Yada Labaran Karamar Hukumar Murtala Umar Kawo ya fitar yace, Shugaban karamar hukumar ya kara da cewa karamar Hukumar Sumaila za ta ci gaba da marawa gwamnan baya wajen aiwatar da shirye shiryen da za su kara inganta al’umma tare da tabbatar da cewa dukkan manufofin gwamnati sun sauka yadda ya kamata a matakin ƙananan hukumomi.

A karshe ya yi addu’ar Allah ya kara tsare Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba shi ikon ci gaba da gudanar da jagoranci na gaskiya da rikon amana tare da samun karin nasarori a dukkan aikace aikace.

 

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles