Daga Wakilin Mu
Bayan gurfanar da wanda ake zargin, Jabiru Umar Sanda Zage, a gaban Kotun Lamba 44 da ke Gwammaja, Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Muhammad Alhaji Isa, kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekara daya kan laifin mallakar kayan maye, da kuma wata shekara daya kan laifin ajiye mata a dakinsa.
Lauyan da ya gabatar da wanda ake zargin a gaban kotu, Auwal Abdulkadir Sani Esq., ya bayyana cewa jami’an kwamitin sun kama Jabiru ne bayan sun gano kwalaben kodin 151 a dakinsa tare da wasu mata uku da ake zargin suna cikin maye.
An gurfanar da shi bisa zargin aikata laifuka da suka hada da shiga harkokin masu aikata laifuka, ta’ammali da kayan maye, bai wa wasu mafaka, da kuma damun jama’a.
Sai dai kotun ta yanke hukuncin ne kan laifukan da suka shafi mallakar kayan maye da kuma ajiye mata a dakinsa, yayin da ba a samu cikakken bayani kan ko za a yi zaman hukuncin ne lokaci guda ko kuma daya bayan daya ba.
Kwamitin Kar-ta-kwana na Yaki da Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi da Daba a Kano ya ci gaba da bayyana aniyarsa ta dakile yaduwar miyagun kwayoyi da sauran ayyukan da ke barazana ga tsaro da zaman lafiyar al’umma.
