Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano Ya Yaba wa Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Kan Bin Umarnin Tsaro

Daga Wakilin Mu

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yabawa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, bisa girmama doka da kuma ci gaba da bin umarnin hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

 

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa Sarkin a fadarsa da ke Nasarawa a Kano. Ziyarar ta biyo bayan wasiÆ™ar sanarwa da Mai Martaba Sarkin ya aika wa hukumomin tsaro, yana bayyana aniyarsa ta gudanar da hawan doki zuwa Yakasai domin halartar bikin saukar karatun AlÆ™ur’ani mai girma.

 

Da yake jawabi a fadar Sarkin, CP Bakori ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce roÆ™on Mai Martaba da ya dakatar da shirin hawan dokin saboda maslahar zaman lafiya da kare lafiyar jama’a. Ya ce duk da cewa hukumomin tsaro sun bukaci masu shirya hawan doki ko Durbar su bayar da sanarwar rubuce aÆ™alla sa’o’i 72 kafin gudanar da taron, halin da ake ciki ya sa ya zama wajibi a nemi a soke shirin baki É—aya.

 

Kwamishinan ya roƙi Sarkin da ya tafi wurin taron ta mota kamar yadda ya saba yi a wasu lokuta, yana mai jaddada cewa hakan zai taimaka wajen kauce wa duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali ko barazana ga zaman lafiyar Kano.

 

CP Bakori ya bayyana Sarkin Aminu Ado Bayero a matsayin shugaba mai bin doka da oda, wanda a kodayaushe yake mutunta umarnin hukumomin tsaro tare da ba zaman lafiya fifiko. Haka kuma ya yi kira ga Alhaji Aminu Babba Dan’agundi, Sarkin Dawaki Babba kuma Babban Mai Ba Sarki Shawara, da ya ci gaba da ba Sarkin goyon baya tare da Æ™arfafa haÉ—in kai da hukumomin tsaro.

 

A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gode wa Kwamishinan da tawagarsa bisa ziyarar, tare da tabbatar musu da cikakken haɗin kansa. Ya ce zaman lafiya, kwanciyar hankali da tsaron Kano su ne abin da ya fi ba muhimmanci, kuma zai ci gaba da mara wa duk wani ƙoƙarin tabbatar da doka da oda baya.

Wannan ziyara na daga cikin matakan da hukumomin tsaro ke ɗauka na ƙarfafa tattaunawa da haɗin gwiwa da cibiyoyin gargajiya domin tabbatar da zaman lafiya da hana duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali a Jihar Kano.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles