Tallafa wa Wadanda Ba Su da Ƙarfin Yin Aure Halas Ne Kuma Yana Cikin Sunnar Annabi (S.A.W.)

Tallafa wa Wadanda Ba Su da Ƙarfin Yin Aure Halas Ne Kuma Yana Cikin Sunnar Annabi (S.A.W.)

Daga Wakilin Mu

Babban Limamin Garin Ghari, Sheikh Imam Nazifi Abubakar, ya yi bayani kan halaccin tallafa wa mutanen da ba su da ikon yin aure, musamman dangane da Shirin Auren Zawarawa da Marasa Ƙarfi da Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar a makon da ya gabata.

Sheikh Imam Nazifi Abubakar ya bayyana cewa babu wata shakka a cikin addinin Musulunci cewa taimaka wa matasa da sauran mutanen da ba su da ƙarfin tattalin arziki domin su yi aure aiki ne mai tushe tun daga zamanin Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam).

Malamin ya kafa hujja da ayoyi daga Alƙur’ani Mai Girma da Hadisan Manzon Allah (S.A.W.), inda ya bayyana cewa koyarwar Musulunci ta amince da tallafa wa waɗanda ba su da ikon yin aure.

Sheikh Imam Nazifi ya kuma yi Allah-wadai da masu sukar Shirin Auren Gama-gari, yana mai cewa ba su da hujja mai ƙarfi ta yin hakan, domin shirin da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ƙaddamar yana da manufar tallafa wa matasa, zawarawa da ‘yan mata domin su samu damar kafa iyali cikin mutunci.

A ƙarshe, Babban Limamin ya yaba wa Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da kuma Gwamnatin Jihar Kano bisa gudanar da Shirin Auren Gama-gari da sauran ayyukan alheri da suke aiwatarwa a birane da ƙauyukan jihar.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles