Karamar Hukumar Ghari Ta Inganta Samar da Ruwan Sha a Mazabu Goma

Karamar Hukumar Ghari Ta Samar da Rijiyoyin Tuƙa-Tuƙa da Fanfunan Hasken Rana Domin Magance Matsalar Ruwa a Mazabu Goma

Daga Shibili Rabiu Sabon Riti

Karamar Hukumar Ghari karkashin jagorancin Shugabanta, Hon. Hashimu Garba Mai Sabulu, ta aiwatar da manyan ayyukan samar da ruwan sha a fadin mazabu goma na karamar hukumar, domin tabbatar da wadataccen ruwan sha mai tsafta ga al’umma.

Da yake bayani kan nasarorin da aka samu a bangaren ruwa, Kansilan Ruwa na Karamar Hukumar Ghari, Hon. Adda’u Haruna Hugungumai, ya ce tun bayan hawan Hon. Hashimu Garba Mai Sabulu kan karagar shugabanci, an samu gagarumin sauyi wajen magance matsalar rashin ruwan sha da ta dade tana addabar al’ummar yankin.

Ya bayyana cewa daga cikin matakan farko da gwamnatin karamar hukumar ta dauka akwai gyaran dukkan rijiyoyin tuƙa-tuƙa da suka lalace a mazabu goma, tare da dawo da su aiki domin saukaka wa jama’a wahalar neman ruwa.

Hon. Adda’u ya kara da cewa gwamnatin karamar hukumar ta samar da sabbin boreholes guda 23, sannan ta gina rijiyoyin tuƙa-tuƙa guda 20 masu amfani da hasken rana, domin fadada hanyoyin samar da ruwan sha mai inganci ga al’ummar Ghari.

Hakazalika, ya ce an gudanar da aikin zamanantar da Gidan Ruwan Ridawa, wanda hakan zai kara inganta samar da tsaftataccen ruwan sha ga mazauna yankin. Ya kuma bayyana cewa al’ummar garin Baje, wadanda suka shafe shekaru suna fuskantar matsalar ruwan sha, yanzu sun samu sauki sakamakon wannan aiki da gwamnatin Hon. Hashimu Garba Mai Sabulu ta aiwatar.

Kansilan ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano bisa ci gaba da tallafa wa kananan hukumomi wajen aiwatar da ayyukan raya karkara, musamman a bangaren samar da ruwan sha da inganta rayuwar al’umma.

A karshe, Hon. Adda’u Haruna Hugungumai ya mika godiyarsa ga Shugaban Karamar Hukumar Ghari, Hon. Hashimu Garba Mai Sabulu, bisa jajircewarsa da kyakkyawan shugabanci, wanda ya haifar da aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba da suka shafi rayuwar al’ummar karamar hukumar.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles