Karamar Hukumar Malunfashi Ta Yabawa Gwamnatin Kano Kan Inganta Tsaro a Lakwaya
Daga Maikudi Muhammad Marafa
Mazauna garuruwan Dansarai da Gidan Buris da ke Karamar Hukumar Manunfashi a Jihar Katsina, wadanda ke makwabtaka da garin Lakwaya na Karamar Hukumar Gwarzo a Jihar Kano, sun kai ziyarar godiya ga Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo, Dr. Mani Tsoho Gwarzo, bisa kokarinsa wajen inganta tsaro a yankin.
A Wata Sanarwa da Jami’in Yada Labaran Karamar Hukumar Gwarzo Yusuf Isyaku ya fitar yace, Jagoran tawagar, Kansilan Mazabar Dansarai, Salisu Rabiu, ya bayyana cewa al’ummarsu na matukar farin ciki da yadda aka samu ingantaccen tsaro a Lakwaya, wanda ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali har ma ga yankunan makwabta. Ya yaba da kokarin Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna, Engr. Abba Kabir Yusuf, wajen tabbatar da tsaro a yankin.
Haka kuma, daya daga cikin wakilan tawagar, Ali Ala, ya jaddada aniyarsu ta ci gaba da bai wa hukumomin Gwarzo hadin kai domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da tsaro.
Da yake mayar da martani, Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo, Dr. Mani Tsoho Gwarzo, ya tarbi bakin cikin girmamawa tare da gode musu kan wannan ziyara, yana mai bayyana jin dadinsa bisa yadda makwabtan ke nuna gamsuwa da kokarin da ake yi. Ya bayyana cewa, karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, an gina gidaje guda biyu tare da samar da ruwa da wutar lantarki domin saukaka wa jami’an tsaro a Lakwaya, tare da samar da motocin aiki da sauran kayan aiki domin karfafa sintiri dare da rana.
Shugaban ya kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai, musamman ta hanyar bayar da sahihan bayanan sirri domin dakile duk wata barazana ga zaman lafiya.
A karshe, Kansilan Mazabar Lakwaya, Hon. Abdul’aziz Isah Kakarya, ya mika godiya ga Gwamnatin Jihar Kano da Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo bisa kokarinsu wajen magance matsalolin tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin da makwabtansa
