
Daga Bello Shehu Shanono
Shugaban karamar hukumar Bagwai Alhaji Bello Abdullahi Gadanya ya bayyana hakan ne lokacin da Yake Jagorantar Ma’aikata dan Kaddamar da Aikin tsaftace Sakatariyar Karamar Hukumar .
Alhaji Bello Abdullahi Gadanya ya nuna muhimmancin da Tsafta take da shi Inda Ya Baiyanata da Cewa itace cikon Addinin musulunci kana ya Jaddada kudurin Majalisarsa na tabbatar da cewa ma’aikatan karamar hukumar Na gudanar da Aiyukansu Cikin Walwala da Jin Dadi.
Shugaban ya kuma tabbatar da cewa Majalisar Karamar Hukumar zata Samar da Wadataccen Ruwan Sha a loko da sako na Yankin Ciki harda Sakatariyar Karamar Hukuma Tare da dawo da Aikin dasa filawowi a Cikinta dan kawatata, kana ya yi Fatan Alkhairi ga Daukacin mahalarta Taron .
A jawabinsa tun da fari shugaban kungiyoyin Aiyukan Gayya na Yankin Kwamarad Ashiru Wakili Sare- Sare ya baiyana farin cikinsa da Jin dadi na ganin Yadda ma’aikatan suka amsa Kira, tare da jinjinawa Shugaban Karamar Hukumar Bagwai Alhaji Bello Abdullahi Gadanya Bisa tiri tiri da Yake yi da daukacin Kungiyoyin Aiyukan Gayya, da Kuma ganin an tsaftace Sakatariyar Mulki ta Karamar Hukumar.
Da Take Jawabi Shugabar Sashen Walwala da Jin Dadin Al-uma ta Yankin Hajiya Zainab Wadda Mataimakinta Ya Wakilta Alhaji Murtala Abdullahi Bichi ya Yabawa Shugaban Karamar Hukumar, Kuma Marafan Bagwai Alhaji Bello Abdullahi Gadanya Sakamakon Goyon Baya da gudunmawar da Yake baiwa sashen ba dare ba Rana dan ganin an Kyautata Walwala da Jin dadin Ma’aikatan Yankin.
Sauran Wadanda Suka gabatar da Jawabai lokacin Taron sun hada da Shugaban Jam’iyar NNPP rashen Karamar Hukumar Bagwai Alhaji Mas’ud Badau, Da Kansilar dake Kula da Sashen Walwala da Jin Dadin Al-uma ta Yankin Hajiya Rabi Sani Bagwai, a Inda Makadan Maza, da Makadan Shantu Suka baje kolinsu lokacin gudanar da gangamin Aikin tsaftace Sakatariyar Mulki ta Karamar Hukumar.
Shehu Bello Shanono
Matemakin Jami in yada labarai
Karamar Hukumar Bagwai

