19.2 C
Kano
Tuesday, January 27, 2026

“Zamu Ɗaga Likkafar Asibitin  Garin Ya daɗi Zuwa Babban Asibiti” Inji Kwamishinan Lafiya

Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano Dakta Abubakar labaran shine

Daga  Shibili Rabi’u Sabon Titi

Gwamnatin jihar Kano za ta daga likkafar asibitin garin yan dadi  da ke yankin karamar hukumar Ghari zuwa Babban asibiti

Kwamishinan Lafiya na jihar Kano Dakta Abubakar labaran shine ya tabbatar da hakan ta bakin wakilinsa


Daraktan Kula da tsaratsare da shirye shirye na maaikatar lafiya Gambo Ya’u Idris. a lokacin da ya ziyarci Asibitin garin yan dadi domin duba gyaran aiyukan asibitin

Ya kuma kara da cewa gwamnatin Enginer Abba kabir yusuf ta damu kwarai da gaske wajen kula da sha’anin harkokin Lafiya a fadin Jihar kano

A nasa jawabin shugaban karamar hukumar ta Ghari Hashim Garba Mai sabulu wanda ya samu wakilcin sakataran karamar hukumar Hashimu Sulaiman ya yabawa Gwamnatin Abba kabir  bisa irin aikace aikacan da ta ke aiwatarwa a karamar hukumar Ghari na Samar musu da hanyoyi da titina da kuma  daga darajar asibitin garin yan dadi zuwa babban asibitin yankin.

Shima da yake jawabinsa kansilan kula da harkokin Lafiya na yankin ya godewa  gwamnana Abba kabir yusuf da ma’aikatar Lafiya ta jihar Kano a karshe kuma ya jinjinawa shugaban karamar hukumar Hashim Mai sabulu yadda ya tsaya tsayin daka har aka samu wan’nan nasara.

Shibili Rabi’u Sabon Titi
Jami’in Yaɗa labarai na karamar hukumar Ghari

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles