Sarkin Rano Ya Kara Jaddada Muhimmancin Yin Rajistar Katin Zabe
Daga Wakilin Mu
An sake jaddada bukatar dake akwai ga mata da Maza wadanda shekarun su ya Kai goma Sha takwas zuwa sama dake yankin masarautar Rano dasu gaggauta yin rijistar katin yin zabe bisa mahimmancin dake tattare da yin hakan.
Mai Martaba Sarkin Rano Ambassada Dr. Muhammad Isa Umaru Autan Bawo na 19 ne yayi wannan Kiran cikin Wani jawabi daya gabatar yayin bikin walimar Saukar dalibai Maza da mata da makarantar madarasatul Ulumudden Islamiya Rano Tsohon Gari ta shirya.
Karanta: KARAMAR HUKUMAR SUMAILA TA TAYA GWAMNAN KANO MURNAR LASHE LAMBAR GIRMAMAWA
Sarkin na Rano Wanda ya dauki Wani tsahon lokaci yana jawabi kan mahimmancin mallakar shi ainishin katin yin zabe, inda yace, bawai kawai ga yin zabe ba kawai, yin ita wannan rijistar katin zaben nada matukar mahimmanci bisa la’akari da irin bukatun da sukan taso a bukaci yin amfani da katin walau wajen cike takardun tafiya yin kartau ko banki ko wutar nefa ko asibiti da dai sauran su, ya dace jama’ar masarautar su Kara fadaka fitowar yin katin.
Ambassada Dr. Muhammad Isa Umaru, ya Kuma fadi cewa haka Kuma hukumar kasa na iya amfani da yawan adadin mutanen da sukayi wannan katin a gari a wajen kason arzikin kasa.
Koda yake jawabi kan ita Saukar ta wadannan dalibai karo ta shid ( 6 ), Sarkin ya bukaci iyaye Maza da Mata dasu dafawa kokarin gwamnati na inganta rayuwa ‘ya’ya ta hanyar mallakar ilimin zamani dama na addini mai inganci ta domin sanin yadda za’a tun Kari Ubangiji.
Koda yake magana kan warware matsalolin makarantar, Sarkin na Rano ya sha’alwashin gina bandakunan Maza da Mata makarantar tare da basu manyan taburmi goma da Kuma tsabar kudi ga kwamatin gudanar da ita makarantar.
Daya juya ga masu Saukar, Mai Martaba Sarkin Rano Ambassada Muhammad Isa Umaru, ya bawa kowanne mai sauka namiji yadin shadda biyar da kudin dinki Yayin Suma mata aka bawa kowacce turmin atamfa da kudin dinki.
Yace kofar masarautar ta Rano na bude dan ganin ana ci gaba da taimakwa addinin musulinci a duk fadin masarautar.
Sarkin na mai godewa malamai da iyayen yara dake makarantar bisa jajircewar su ta bawa yara ilimi mai inganci.
Cikin jawabin shugaban makarantar malam Lawan Umar yace makarantar an kafata sama da shekaru sittin, a halin yanzu tana da dalibai sama da dari uku da ashirin.
Kuma makarantar nada matsalolin rashin bandakunan dalibai bayan tarin nasarori data samu.
Dan majalisar wakilai na kasa dake wakiltar kananan hukumomin Rano da Bunkure da kuma kibiya a majalisar wakilai Honarabil Kabiru Alhassan Rurum Wanda ya Sami wakilcin Tsohon sakataren ilimi na Rano Alhaji Abbulhadi Tijjani Rano ya bawa makarantar taimakon na’uarar bada hasken wuta ta solar dan inganta tsaro, inda su Kuma dalibai masu Saukar ya basu naira biyar kowannan su. A inda shugaban karamar hukumar Rano Alhaji Naziru Ya’u ya bada gudunmawar naira dubu hamsin ga hukumar makaranta.
Sa Hannu,
Nasiru Habu Faragai,
Sakataren Yada Labaran,
Masarautar Rano.

