
Daga: Umar Abdu Kurmawa
Sabon Shugaban Hukumar Fansho na Jihar Kano Alhaji Habu Ibrahim Fagge ya Kama aiki gadan-gadan.
Alhaji Habu Muhammad Fagge ya fara gudanar da aikin nasa ne ta Kai ziyara ta musammam ga ofishin kungiyar yan fansho ta Jihar Kano da Kuma Kai ziyara ga wasu daga cikin kadarorin Hukumar da suka hadar da wadanda ke kan titin Panshekara da rukunin Gidajen Kwankwasiyya dake karamar Hukumar Kunbotso inda sabon shugaban Hukumar ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Kano karkashin Jagorancin Engineer Abba Kabir zata bada kulawa ga yan fansho dake fadin Jihar Kano.

A Jawabin Shugaban kungiyar yan fansho ta jihar Kano Kwamarid Salisu Ahmed Gwale yabawa Kwamnan Jihar Kano yayi bisa kawò Alhaji Habu Muhammad Fagge musamman yadda yasan aiki da Kuma kwarewa a bangaren harkokin kudi Tare da yin Alkawarin bashi goyan baya Dari bisa Dari Haka.

Shima da yake Jawabi Shugaban Æ™ananan ma’aikata da manya na Hukumar Fansho Sadik Sidi Kabara yace sun gudanar da adduo’Ä« na musamman ga sabon shugaban shugaban nasu tare da nuna farin cikinsu matuka da zuwan sa.
Daga bisani Babban Sakatare a Hukumar Alhaji Nuhu Dambatta ya bukaci daukacin Ma’aikatan Hukumar dasu kula da zuwa Aiki da Wuri harma da bin duk wasu dokokkin Gwamnatin Jihar Kano domin ciyar da yan Fansho Gaba.

