21.3 C
Kano
Tuesday, January 27, 2026

“Mun Kuduri Aniyar Yakar Matsalar Tsaro a Karamar Hukumar Rogo” Inji Mustapha Rogo

Shugaban Karamar Hukumar Rogo, Alhaji Abubakar Mustapha Rogo

Daga Abdu Bako Abdullahi

Shugaban Karamar Hukumar Rogo, Alhaji Abubakar Mustapha Rogo, ya tabbatar da cikakken kudurinsa na yaki da ‘yan bindiga tare da tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da mutanen Nasarawa wadanda suka kawo masa ziyarar ta’aziyya sakamakon rasuwar Hakimin Nasarawa, Alhaji Umar Bello.

Taron ya gudana ne a Sakateriyar Karamar Hukumar ta Rogo.

A jawabin nasa, Alhaji Abubakar Mustapha Rogo ya yi kira ga al’ummar yankin da su cigaba da zama cikin lumana da bin doka, tare da tabbatar musu da cewa karamar hukumar tana aiki tukuru wajen samar da tsaro mai inganci a fadin yankin.

Ya godewa jama’a bisa goyon bayan da suke bayarwa, tare da yin addu’ar zaman lafiya ya tabbata a yankin.

Haka kuma, ya jaddada goyon bayansa ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wajen cimma manufofin gwamnati na tsaro.

A nasa bangaren, Mukaddashin Dagaci Nasarawa, Malam Murtala Isma’il, ya yaba wa Shugaban Karamar Hukumar da Majalisar sa bisa jajircewarsu wajen inganta harkar kiwon lafiya da tsaro a yankin.

Ya tabbatar wa karamar hukumar da goyon bayan al’ummar Nasarawa tare da mika ta’aziyya kan rasuwar marigayi Dagaci Alhaji Umar Bello.

Taron ya samu halartar manyan jami’an karamar hukumar, ciki har da Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar, Yahaya Shu’aibu Yunusa Madatai; Sakataren Karamar Hukumar, Basiru Magaji Beli; Shugaban Majalisar Kansiloli, kansiloli, masu ba da shawara, masu kula da bangarori daban-daban, da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar NNPP.


Abdu Bako Abdullahi
Jami’in Yada Labarai na, Karamar Hukumar Rogo.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles