26.6 C
Kano
Monday, January 26, 2026

Masarautar Rano Ta Sake Nanata Kudirin Ta Na Cigaba Da Yaki Da Hana Shan Miyagun Kwayoyi A Tsakankanin Matasa

 

Masarautar Rano Ta Sake Nanata Kudirin Ta Na Cigaba Da Yaki Da Hana Shan Miyagun Kwayoyi A Tsakankanin Matasa

Daga Nasiru Habu Faragai

Masarautar Rano Ta Sake Nanata Kudirin Ta Na Cigaba Da Yaki Da Hana Shan Miyagun Kwayoyi A Tsakankanin Matasa da sauran jama’ar dake ta’amali da miyagun kwayoyin a
duk fadin masarautar.

Mai Martaba Sarkin Rano Ambasada Muhammad Isa Umaru ne ya furta hakan cikin Wani jawabi daya gabatar lokacin da yake amsar bakuncin kungiyar Mai radin wayar da Kan al’umma Kan illar dake tattare da Sha da ka fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar nan yau laraba 28/5/25 da kungiyar ta kawo masa a fadar sa.

Sarkin na Mai sake tabbatarwa hukumar ta hana Sha da fataucin kwayoyi ta kasa cewar har kowane lokaci kudirin masarautar Rano ne taga cewa matasan masarautar sun zanto abin koyi ta fuskar kyakkyawar tarbiya a duk inda suke.

Ambasada Muhammad Isa Umaru yana Mai godewa hukumar hana Sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa da Kuma reshen jiha bisa tuna nin su na ziyartar fadar da nuna yabawa da Kuma godiyar su bisa ga irin gudunmawar da Sarkin ke yi wajen fadakar da matasa tare da shirya wasannin kwallon kafa tsakanin matasa dan kautar da tunanin su Kan kaucewa Shan irin wadannan kwayoyi.

Da yake jawabi tun da farko shugaban kungiyar Hana Sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jiha Honarabil Salisu Sa’adu Lili yace sun ziyarci Sarkin da nufin yi masa ta’aziyar batuten ‘yan sandan da Kuma matashin da suka rasu bisa iftila’i daya faru a Rano.

Haka Kuma kungiyar ta ce sunzo fadar domin bayyana godiya da yabawar hukumar Kan yadda suke samun rahotannin gudunmawar Sarkin Kan yaki da Hana Shan miyagun kwayoyi tsakankanin matasan dake masarautar ta Rano.

Sun Kuma ce nan kusa zasu shirya wata bita a masarautar da nufin hada Kan matasa da Kuma yaki da Hana Shan miyagun kwayoyi tsakankanin matasan yankin.

A dai wannan ranar ta yau Sarkin ya karbi bakuncin Babban daraktan gudanarwa na bankin access Alhaji Aminu Inuwa Taura Kuma Galadiman Tauran a shirye shiryen amincewar bankin na bude Sabon reshen a garin Rano.

Nasiru Habu Faragai, Sakataren yada Labaran Masarautar Rano.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles