21.3 C
Kano
Tuesday, January 27, 2026

Kungiyar Cigaban Unguwar Sabon Gida Ta Taya Muhuyi Magaji Rimin Gado Murna

Daga: Aliyu Marafa


TAYA BARRISTER MUHUYI MAGAJI RIMIN GADO MURNAR KOMAWA AIKINSA NA SHUGABAN HUKUMAR KARBAR KORAFE-KORAFE DA YAKI DA CIN HANCI DA RASHAWA NA JIHAR KANO.


Kungiyar Cigaban Al’ummar Unguwar Sabon Gida dake Yankin Ć™aramar Hukumar Gwale ta taya Malam Muhuyi Magaji Rimin Gado murnar komawa aikinsa na Shugaban hukumar Korafe- Korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa na Jihar Kano .


A cikin wata takardar sanarwa mai dauke da sa hannun daya daga cikin yan kungiyar Alh Nura I. Yakasai ta bayyana cewar “Muna amfani da wannan dama, a Madadadin Shuwagabanni da Al’ummar wannan Ć™ungiya ta Cigaban Al’ummar Sabongida, wajen taya Dan’uwa, Makoci kuma Mai ai kishin wannan Unguwa da kewaye, Barrister Muhuyi Magaji Rimin Gado murnar samun damar komawa kan kujerar sa ta shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano.”


Muna tare da Barrister Muhuyi Magaji Rimingado a wannan dandali kuma ya na bayar da dukkan gudunmowa domin cigaban wannan yanki.


“Muna fatan wannan dama da ya samu za ta zama wata sila da al’ummar wannan yanki za su yi alfahari da shi.”


*Allah Ya Yi masa jagoranci, Ya Bashi ikon sauke nauyin da aka dora masa Ameen”.

Alhaji Nura I. Yakasai

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles