26.6 C
Kano
Monday, January 26, 2026

ĶARAMAR  HUKUMAR  GARKO TA SAMI DAMA MAI YAWA NA MUKAMAI DA AYYUKAN CI GABAN BIL ADAMA A CIKIN SHEKARU BIYU NA MULKIN GWAMNA ABBA KABIR YUSUF — IN JI SAKRATARIN ĶARAMAR  HUKUMAR  GARKO 

ĶARAMAR  HUKUMAR  GARKO TA SAMI DAMA MAI YAWA NA MUKAMAI DA AYYUKAN CI GABAN BIL ADAM A CIKIN SHEKARU BIYU NA MULKIN GWAMNA ABBA KABIR YUSUF — IN JI SAKRATARIN ĶARAMAR  HUKUMAR  GARKO

Ķaramar Hukumar Garko ta sami damar yin amfani da mukamai da yawa da kuma ayyukan ci gaban bil adama a cikin shekaru biyu na mulkin Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Shugaban karamar hukumar Garko, Hon. Saminu Abdullahi, ya bayyana haka ta hannun Sakataren Karamar Hukumar, Alhaji Garba Inusa Mai Salati, a wani taron manema labarai.

Saminu Abdullahi ya ce tun lokacin da aka fara mulkin dimokuradiyya, babu wata gwamnati da ta baiwa mutanen Garko  mukamai kamar na Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya kara da cewa, dangane da ayyukan da suka dace da rayuwar al’umma, gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta gudanar da ayyuka masu mahimmanci da yawa Waɗanda sun haɗa da haɓaka Asibitin Garko zuwa Babban Asibiti, gina hanyar kilomita 27 daga Danin zuwa Dan Hausa har zuwa garin Garko, gina magudanan ruwa a Dam din Kafin Ciri don inganta noman damina, aikin gina hanyar kilomita 5, kafa cibiyar horar da mata da koyon karatu, da kuma tallafin kuɗi na ₦50,000 ga mata ɗari a kowane wata.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta ba wa karamar hukumar damar aiwatar da ƙarin ayyuka, kamar gina makarantu a garuruwan Garko da Dan Maliki, gyara asibitoci shida a garuruwan Lamire, Garin Ali, Garwaji, gina hanyar daga Kwanar Lamire zuwa tsakiyar gari, da kuma gyara rijiyoyin da suka lalace a dukkan unguwanni goma na karamar hukumar.

Shugaban ya kuma tabbatar da goyon bayansa ga shugaban Kwankwasiyya, Injiniya Dokta Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf a kowane lokaci.

Ya kuma yi kira ga jama’a su ci gaba da yin addu’a da tallafawa gwamnatin domin ci gaba da samun ribar dimokuradiyya.

Daga:
Auwalu Rabiu Ali,
Jami’in Labarai,
Karamar Hukumar Garko

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles