
Fame Hausa
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya zargi alkalan kotunan kasar da ruguza wajen hukunce hukuncen da suke bayarwa.
Kafar Yaɗa Labarai ta RFI ta bayyana cewar Jonathan ya bayyana wasu daga cikin irin wadannan hukunce hukunce a matsayin wadanda ke sabawa abinda jama’a suka zaba.
Tsohon shugaban ya bukaci alkalai da su dinga nesanta kansu daga harkokin siyasa domin basu damar gudanar da shari’a ba tare da nuna bangare ba.

