Jami’ar MyLes ta Ghana za ta Karrama Sarkin Kano da Digirin Girmamawa
Jami’ar MyLes da ke Jamhuriyar Ghana ta bayyana aniyarta ta karrama Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, da Digirin Girmamawa, bisa gudummawar da yake bayarwa wajen jagoranci nagari, zaman lafiya da ci gaban al’umma.
Shugaban Jami’ar MyLes, Isma’ila Sani Muhd, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyara da tawagar jami’ar ta kai fadar Sarkin Kano da ke Gidan Sarki na Nassarawa. Ya ce sun zo Najeriya ne domin sanar da Mai Martaba Sarkin shirin jami’ar na bashi wannan gagarumar karramawa.
A cewarsa, Sarkin Kano ya cancanci kowace irin lambar yabo da girmamawa sakamakon kishinsa ga al’umma, jajircewarsa wajen tafiyar da harkokin mulki cikin adalci, kaunar zaman lafiya da kuma nuna kulawa ga jama’arsa.
Da yake mayar da jawabi, Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya gode wa tawagar jami’ar bisa wannan ziyara da kuma wannan shiri na karramawa. Ya tabbatar musu da cikakken hadin kai da goyon bayan Masarautar Kano a dukkan abubuwan da suka sanya a gaba.
Sarkin ya jaddada cewa Digirin Girmamawar da za a ba shi ba nasa kadai ba ne, illa na Masarautar Kano da kuma al’ummar Jihar Kano baki daya.
Haka kuma, Sarkin ya yabawa kyakkyawar alakar da ke tsakanin Najeriya da Ghana, tare da kira ga jami’ar da ta ci gaba da kulla alakar hadin gwiwa a fannin ilimi domin ci gaban al’ummomin kasashen biyu.
A karshe, Mai Martaba Sarkin Kano ya sake gode wa tawagar Jami’ar MyLes bisa wannan ziyara da sanar da shi shirin karramawar Digirin Girmamawa.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Sakataren Yada Labarai na Mai Martaba Sarkin Kano
Alhaji Aminu Ado Bayero CFR, JP, CNOL

