Jami’an KAROTA Sun Dakile Harin Wasu Bata-gari a Wata Makaranta a Kano
Daga Maikudi Muhammad Marafa
Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta tabbatar da kudurinta na ci gaba da gudanar da ayyuka na kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a dukkan fadin jihar.
Shugaban hukumar, Hon. Faisal Mahmud Kabir, ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi bakuncin shugabannin Makarantar Sakandiren ’Yan Mata ta Aisha Shehu, dake unguwar Fagge, wadanda suka kai masa ziyarar godiya saboda yadda jami’an KAROTA suka dakile harin wasu bata-gari da suka yi yunkurin satar kayayyaki masu daraja daga makarantar.
A Sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Abubakar Ibrahim Sharada ya bayyana cewar, Hon. Faisal ya yabawa jami’an hukumar bisa jajircewar da suka nuna wajen kare dukiyar jama’a, yana mai cewa wannan aiki ya nuna ƙwazo da kishin kasa.
“KAROTA za ta ci gaba da gudanar da aikinta da cikakken sadaukarwa domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Ayyukan irin waɗannan jami’ai na karfafa mana gwiwa don ƙara himma wajen hidimtawa jama’a,” in ji shi.
Ya kuma godewa shugabannin makarantar bisa ziyarar da suka kawo, inda ya bayyana cewa haɗin kai tsakanin hukumomin gwamnati da al’umma shi ne ginshiƙin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a cikin al’umma.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugabar Makarantar, Malam Maikudi Muhammad Lawan, wanda ya wakilci shugabar makarantar Hajiya Rafa’atu Mahmud Baffa, ya bayyana cewa sun ziyarci KAROTA ne domin nuna godiya bisa yadda jami’an hukumar suka nuna ƙwazo wajen kare kadarorin makarantar daga satar da aka shirya.
“Mun ga dacewar mu kawo ziyara ga KAROTA don nuna godiya bisa yadda jami’anta suka taka muhimmiyar rawa wajen kare kadarorin makarantar. Wannan aiki abin alfahari ne ga duka al’umma,” in ji shi.
Jami’an KAROTA da suka nuna jajircewa wajen wannan aiki sun haɗa da, Aminu Muhammad Bello – Babban jami’i mai kula da Masallacin Fagge, da Nuraddeen Ibrahim Inuwa, Abba Nasidi da kuma Ibrahim.
Hukumar KAROTA ta jaddada cewa za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin kai da sauran hukumomi da jama’a wajen tabbatar da tsaro, inganta zirga-zirgar ababen hawa, da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar Kano.

