“ZAMU TALLAFAWA JAMI’AN TSARO DOMIN GUDANAR DA AIKIN SU A YANKIN” Inji Dr. Chula

“ZAMU TALLAFAWA JAMI’AN TSARO DOMIN GUDANAR DA AIKIN SU A YANKIN” Inji Dr. Chula

Daga: Ibrahim Haladu Gaya

Karamar Hukumar Ajingi ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da tallafawa jami’an tsaro da ke gudanar da aikinsu a yankin.

Shugaban karamar hukumar, Dr. Abdulhadi Zubairu Chula, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi baƙuncin kwamandan rundunar ‘yan sandan Najeriya mai kula da shiyyar Wudil a ofishinsa.

Karanta: Kano State Advances Toward Sustainable Health Development

Dr. Chula ya bayyana cewa zai haɗa kai da sauran shugabannin kananan hukumomi guda shida da ke ƙarƙashin rundunar Wudil domin gyara ofishin rundunar da ke Wudil.

Ya kuma tabbatar wa kwamandan da shirinsa na gyara sabon ofishin ‘yan sanda da ke fuskantar sakatariyar karamar hukumar Ajingi, wanda aka yi watsi da shi a baya.

Dr. Chula ya yaba wa kwamandan ‘yan sandan Ajingi, ASP Abubakar Ladodo, bisa ƙoƙarinsa na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.

A nasa jawabin, kwamandan rundunar shiyyar Wudil, ACP Husaini Yalwa, ya ce ziyararsa ta zo ne domin ƙarfafa alaƙar zumunci tsakanin rundunar ‘yan sanda da karamar hukumar Ajingi.

Read Also: Defence Minister Badaru Attends Nigerian Defence Academy Passing Out Parade 

ACP Yalwa ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da jajircewa wajen yaƙar miyagun da ke tayar da hankalin jama’a a ƙananan hukumomin da ke ƙarƙashinsa shiyyar.

Sauran masu jawabi a wurin taron, ciki har da sakataren karamar hukumar Ajingi, Malam Nazifi Husaini Toranke, da daraktan Mulki da gudanarwa, Alhaji Auwalu Malami, sun bayyana cikakken goyon bayansu domin tabbatar da dorewar zaman lafiya da tsaro a yankin.

 

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles