24.9 C
Kano
Tuesday, January 27, 2026

An jinjinawa Mai Martaba Sarkin Rano Ambasada Muhammad Isa Umaru bisa yadda yakewa addinin musulunci hidimar data dace da buka

17/03/25. EMIRATE.

Majalisar Makarantun Alquar’ ani da Islamiyu ta jiha reshen shiyar Rano ta An jinjinawa Mai Martaba Sarkin Rano Ambasada Muhammad Isa Umaru bisa yadda yakewa addinin musulunci hidimar data dace da bukatun al’ummar musulmi musamman a wannan wata na azumin Ramadan Mai albarka.

Shugaban majalisar Malam Ishak Umar Kofa Bebeji ne ya furta hakan cikin wata ziyara da kungiyar ta kaiwa Mai Martaba Sarkin na Rano yau a fadar sa domin nuna goyon baya tare da neman Sarkin ya sanya musu albarka a fadar sa.

Shugaban Ishak Umar Kofa yace kungiyar ta ziyarci Sarkin Kuma nufin yi masa jawabi Kan irin goyon bayan da yake bawa kungiyar majalisun na Makarantun Alquar’ani da Islamiyu ta fuskar halartar tarrurukan saukar dalibai na Makarantu a duk lokacin da aka gayyace shi kazalika da bada gudunmawar sa na tufafi da kudade ga dalibai Kai harma da malaman da kwamitocin Makarantu da makamantan su.

Haka Kuma kungiyar ta sake jinjinawa Sarkin bisa yadda cikin wannan wata Mai Alfarma na Ramadan yake rarrabawa matan aure da mazaje da marayu turamen atamfuna da yadina da kayan abinci da Kuma kudi duk day nufi rangwantawa musulmi halin rayuwa a wannan wata na Ramadan.

Da yake jawabin amsar bakuncin kungiyar Mai Martaba Sarkin Rano Ambasada Muhammad Isa Umaru, godewa shugabannin kungiyar yayi bisa wannan ziyara tare da Jan hankali su dasu kiyaye da amanar nauyin shugabanci da aka dora musu.

Yana Mai  cewar Kofar masarautar Rano na bude Koda yaushe dan sauraron shawarwari da korafe korafen jama’a dan warware su.

Haka Zalika yau din dai Mai Martaba Sarkin na Rano ya Kuma karbi bakuncin kungiyar jagorori mata na mazabu Goma a karkashin jam’iyar NNPP na karamar hukumar Rano a fadar sa karkashin jagorancin Hajiya Habiba Muhammad.

Hajiya Habiba Muhammad tace sun ziyarci fadar ne da nufin nuna godiya bisa irin yadda Mai Martaba Sarkin Rano ke tallafawa mata Akai Akai cikin wannan wata na Ramadan.

Tace farko Azumi an basu kayan Shan ruwa yanzu Kuma an rabawa mata sama masu yawa turamen atamfofi da kudin dinki kowannan su.

Da yake jawabi Mai Martaba Sarkin Rano Ambasada Muhammad Isa Umaru ya bayyana gamsuwar sa bisa yadda shugabannin mata ‘yan jam’iyar NNPP ke bawa gwamnatin jiha hadin Kai da goyon baya dan kuma fadakar da jama’a a Sami sukunin gudanar da aikace aikace da Kuma mahimmancin samun zaman lafiya.

 

 

 

Nasiru Habu Faragai

Sakataren Yada Labaran Masarautar Rano.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles