24 C
Kano
Monday, January 26, 2026

An Bayyana Bukatar Amincewar Karin Ayyukan Ci Gaba Ga Gwamnatin Jihar Kano A Karamar Hukumar Dambatta 

An Bayyana Bukatar Amincewar Karin Ayyukan Ci Gaba Ga Gwamnatin Jihar Kano A Karamar Hukumar Dambatta

Daga Tasiu Jimbo Dawanau

An yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf da ya amince da ƙarin ayyukan ci gaba da ƙaramar hukumar Dambatta ta tura masa domin dorewar ci gaban al’ummar yankin.

Wani mazaunin yankin, Abdulbasi Abdulrazzak Shiddar, ne ya yi wannan kira yayin da yake bayani kan shirin tallafawa mata da matasa na wata-wata da ƙaramar hukumar Dambatta ke aiwatarwa.

Ya bayyana cewa shugaban ƙaramar hukumar yana raba wa mata da matasa ɗari adadin kudi naira dubu ɗari-dari(₦100,000) kowannensu domin taimaka musu su zama masu dogaro da kansu a harkokin rayuwa.

Abdulbasi ya ƙara da cewa mataki na biyu na gyaran sakatariyar ƙaramar hukumar Dambatta yana ci gaba, wanda nufin sa shi ne samar da yanayi mai kyau domin aiki, da kuma ƙarfafa ma’aikata su jajirce wajen hidimtawa jama’a.

Karanta: “ZAMU TALLAFAWA JAMI’AN TSARO DOMIN GUDANAR DA AIKIN SU A YANKIN” Inji Dr. Chula

A nasa bangaren, mai baiwa shugaban ƙaramar hukumar shawara kan al’amuran siyasa, Musa Muhammad Nayari, ya bayyana cewa Alhaji Jamilu Abubakar ya raba babura guda goma sha shida (16) ga shugabannin jam’iyyar NNPP na Mazabu goma, tare da wasu ‘yan jam’iyya guda shida da suka sadaukar da kansu wajen aiki tukuru, a matsayin kayan tallafi .

Yace izuwa wannan lokacin shugaban Majalisar karamar hukumar ya Raba Baburan Hawa guda Sittin ga Matasa domin su dogaro da kansu.

Musa Muhammad Nayari ya nuna godiya bisa wannan karamci, tare da shawartar al’ummar yankin da su ci gaba da yin addu’a domin samun ƙarin ayyukan ci gaba a cikin mazabu goma na ƙaramar hukumar ta Dambatta.

 

Related Articles

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles