“Zamu Ci Gaba Da Tallafawa Kungiyoyin Cigaban Al’umma”- Inji Ibrahim Kabara

Gwamnatin Jihar Kano Ta Sake Jaddada Goyon Bayanta ga Ƙungiyoyin Raya Al’umma a Ƙananan Hukumomi 44 Na JIHAR

Daga Maikudi Muhammad Marafa

Gwamnatin Jihar Kano ta sake tabbatar da aniyarta na ci gaba da tallafa wa mambobin Kwamitin Gudanarwa na Jiha na Ƙungiyoyin Raya Al’umma (Central Working Committee on Community Development Organizations) da ke faÉ—in Æ™ananan hukumomi 44 na jihar.

A wata Sanarwa da Jami’an Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Farouk Ghali Masanawa ya fitar ya Bayyana cewar Sakataren Dindindin na Ma’aikatar Raya Karkara da Ci gaban Al’umma, Alhaji Ibrahim Muhammad Kabara, ne ya bayyana hakan yayin da yake karÉ“ar baÆ™uncin mambobin Kwamitin Gudanarwa na Jiha a ofishinsa.

Alhaji Ibrahim Muhammad Kabara ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware makudan kuÉ—aÉ—e domin samar da kayayyakin aiki ga Ƙungiyoyin Taimakon Kai (Self-Help Groups) a dukkan Æ™ananan hukumomi 44 na jihar. Ya ce wannan mataki na daga cikin Æ™oÆ™arin gwamnati na bunÆ™asa ci gaban karkara tare da Æ™arfafa al’umma su taka rawar gani wajen ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.

Ya gode wa kwamitin bisa wannan ziyarar, tare da tabbatar musu da shirinsa na yin aiki kafada da kafada da su domin cimma manufofin ma’aikatar da kuma Æ™ara inganta ci gaban karkara da al’ummomin Jihar Kano.

Alhaji Ibrahim Kabara ya kuma buÆ™aci mambobin kwamitin da su ci gaba da yi wa gwamnatin Jihar Kano addu’ar samun nasara a Æ™arÆ™ashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da fatan gwamnatin za ta ci gaba da samun nasarori a ayyukan raya jihar.

Tun da farko, Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Jiha, Alhaji Ibrahim Aminu Kofar Na’isa, ya bayyana cewa sun kai ziyarar ne domin taya Alhaji Ibrahim Muhammad Kabara murnar nadin da aka yi masa tare da tura shi Ma’aikatar Raya Karkara da Ci gaban Al’umma a matsayin Sakataren Dindindin.

Ya kuma tabbatar da cikakken goyon baya da haÉ—in kan kwamitin ga gwamnatin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, yana mai jaddada aniyarsu ta ci gaba da haÉ—a hannu da gwamnati wajen bunÆ™asa ci gaban karkara da al’ummomin Jihar Kano.

 

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles