
Daga Maikudi Muhammad Marafa
An bukace daukacin ma’aikatan hukumar kula da gyaran tituna ta jihar Kano dasu zamantu masu jajirciwa wajen gudanar da ayyukan su.
Sabon Manajan daraktan hukumar Kula da Gyaran Tituna Alhaji Hassan Danbaffa ne ya bayyana bukatar hakan lokacin da yake karbar ragamar shugabancin hukumar.
Alhaji Danbaffa ya bayyana cewar zai gudanar da aikin sa bisa gaskiya da rikon amana bisa la’akari da muhimmancin da hukumar ke dashi domin ciyar da jihar kano gaba ta fannin inganta hanyoyin dake jihar nan.
Ya godiwa gwamnan jihar kano bisa mukamin da aka bashi tare da bayyana kudirin sa na gudanar da aikin sa bisa gaskiya da rikon amana.
Tun da farko a Jawabinsa, Daraktan Mulki da Kudi na Hukumar Alhaji Kabara tabbaci hadin kai da goyan bayan ma’aikatan hukumar ya bayar ga Sabon Shugaban domin samun nasarar gudanar da aikin sa.

