Dimbin Al’umma Sun Halarci Walimar Kammala Aikin Alhaji Mukhtar Aliyu na Hukumar Kwastam a Kano
Daga Wakilin Mu
Al’ummar Unguwar Sabuwar Gandu da makwabtan unguwanni a Jihar Kano sun yi dandazo domin halartar walimar taya murna ga ɗan su, Alhaji Mukhtar Aliyu, bisa kammala aikinsa lafiya a Hukumar Kwastam ta Ƙasa bayan dogon lokaci na hidima mai cike da jajircewa, gaskiya da rikon amana.
An gudanar da walimar ne a ranar Alhamis, 1 ga Janairu, 2025, a Ali Jita Event Centre, da ke kan titin Lawan Dambazau Road, Kano. Taron ya gudana karkashin jagorancin Dr. Ibrahim Muhammad Gandu, tare da Alhaji Anas, Abdullahi Abubakar Bisi da sauran membobin kwamitin dattawan Sabuwar Gandu.
Taron ya samu albarkar halartar iyayan ƙasa, hakimai, masu unguwanni, manyan baki, abokan aiki daga Hukumar Kwastam, da iyalai da masoya Alhaji Mukhtar Aliyu, lamarin da ya nuna yadda al’umma ke girmama jajircewarsa da kyawawan ɗabi’unsa.
An haifi Alhaji Mukhtar Aliyu a shekarar 1969 a Gandun Sarki (Audu Bako Secretariat) a Kano. Ya fara neman ilimin addini tun yana ƙarami, sannan ya haɗa da ilimin boko, inda ya yi karatu a Gandun Nassarawa Primary School, Sabuwar Kofa Junior Secondary School, da Government Technical College Kano, inda ya samu Takardar Kwarewa a Gyaran Lantarki (Electrician).
A shekarar 1991, Allah Ya ba shi aiki a Hukumar Kwastam ta Ƙasa a matsayin Customs Assistant III, bayan ya kammala horo a Makarantar Horon Kwastam ta Kano. A tsawon aikinsa, ya yi hidima a jihohi daban-daban da suka haɗa da Katsina, Kano, Rivers, Enugu, Abuja da Lagos.
Baya ga aiki, Alhaji Mukhtar Aliyu bai daina neman ilimi ba, inda ya samu Certificate of Administration (CA) daga FCE Kano, sannan ND da HND a fannin Kasuwanci da Tattalin Arziki daga Kano State Polytechnic. Wannan ƙoƙari ya ba shi damar samun ƙarin girma daga Assistant Superintendent, zuwa Deputy Superintendent, har zuwa Superintendent of Customs (SC), mukamin da ya kai shekarar ritayarsa a kai.
Alhaji Mukhtar Aliyu mutum ne mai kyawawan ɗabi’u, son cigaban al’umma da taimakon jama’a, tare da kaskantar da kai da ladabi, abin da ya sa yake da matuƙar farin jini a cikin al’umma.

