Shugaban Karamar Hukumar Rano, Naziru Ya’u, Ya Kai Ziyarar Gaisuwa Ga Sarkin Rano
Dakataccen Shugaban Karamar Hukumar Rano, Alhaji Naziru Ya’u Rano, wanda majalisar dokokin Jihar Kano ta dakatar a baya bisa wasu dalilai, ya dawo kan kujerarsa bayan kammala bincike da majalisar ta gudanar, ya kai ziyarar gaisuwa da gabatar da kansa ga Mai Martaba Sarkin Rano a fadarsa.
A jawabinsa yayin ziyarar, Alhaji Naziru Ya’u Rano ya bayyana cewa ya yafe wa kowa da kowa, yana mai cewa zai yi koyi da kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW) wajen yafiya da hada kan al’umma. Ya jaddada cewa ba shi da wani bacin rai a kan kowa a cikin Karamar Hukumar Rano ko ma’aikata da sauran shugabanni.
Shugaban karamar hukumar ya tabbatar wa Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Dakta Muhammad Isa Umaru, cewa zai yi aiki tukuru domin karfafa hadin kai da ci gaban al’umma. Ya ce shugabanin za su yi amfani da wannan damar domin ci gaba da inganta harkokin rayuwa da walwalar jama’a ba tare da nuna bambanci ba.
A nasa bangaren, Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Dakta Muhammad Isa Umaru, ya yaba da irin kokarin da Alhaji Naziru Ya’u Rano ke yi wajen tallafawa masarauta da al’umma. Ya kuma bukace shi da ya ci gaba da gudanar da ayyukan alheri, ciyar da yankin gaba, da kula da jama’a da magoya baya domin tabbatar da zaman lafiya da cigaba a Karamar Hukumar Rano.
Ziyarar ta ja hankalin jama’a da dama ciki har da manyan jagororin jam’iyyar NNPP, ma’aikatan karamar hukuma da magoya baya, wadanda suka rakashi cikin girmamawa zuwa fadarsa.

