24 C
Kano
Monday, January 26, 2026

Gwamnatin Kano Zata Samar Da Lita 75,000 A Kullum Ga Al’ummar Garin Rano

Gwamnatin Kano Zata Samar Da Lita 75,000 A Kullum Ga Al’ummar Garin Rano

Daga Maikudi Muhammad Marafa

Kwamishinan Ruwa na Jihar Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa, ya tabbatar da cewa aikin samar da ruwan sha a Rano – wanda Gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince da shi – zai fara a aikace nan bada jimawa ba.

A Wata Sanarwa da Sakataren Yada Labaran Masarautar Rano Malam Nasiru Habu Faragai ya fitar, ta Bayyana cewar, Kwanishina Doguwa ya sanar da hakan ne lokacin da ya jagoranci tawagar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa fadar Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Dakta Muhammad Isa Umaru. Tawagar ta haÉ—a da Kwamishinar Al’adu, Aisha Lawan Saji Rano, Babban Sakataren Ma’aikatar Ruwa, shugaban kamfanin da aka ba wa kwangila, ‘yan majalisar jiha daga Rano, Kibiya da Bunkure, tare da shugabannin kananan hukumomin Rano, Bunkure da Kibiya.

Karanta: Sadaukarwa Ga Ma’aikatan Wucin Gadin Kafafen Yada Labarai

A yayin ziyarar, Kwamishinan ya bayyana cewa aikin ya ƙunshi samar da ruwa daga Taluwaiwai zuwa tsakiyar garin Rano, wanda zai samar da ruwa ga mutum 75,000 a kowace rana. Haka kuma aikin ya haɗa da gyaran bututun ruwan Tiga zuwa Rano domin tabbatar da cewa matsalar ƙarancin ruwa ta zama tarihi a yankin Rano da makwabtansa.

Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Dakta Muhammad Isa Umaru, ya bayyana godiyarsa ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa amincewa da fara wannan muhimmin aiki da zai amfanar da dubban jama’ar Rano. Ya kuma yaba da yadda gwamnan ke kasancewa a bude ga koke-koken jama’a tare da ɗaukar matakan da suka dace wajen sauƙaƙawa al’umma rayuwa.

Karanta: Ziyarar Bazata: Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso Ya Ziyarci Asibitin Maikalwa 

A tarihin da Sarkin ya tunatar, ya ce :”Idan masu sauraro ba su manta ba, a lokacin Karamar Sallah da na kai gaisuwar sallah ga Gwamnan Jiha, na gabatar masa da koke kan matsananciyar matsalar ruwan sha da al’ummar Rano ke fama da ita. Yau kuma muna ganin amfanin wannan koke.”

Mai Martaba Sarkin ya sake mika godiya ga gwamnan bisa jajircewarsa wajen inganta rayuwar al’ummar masarautar Rano.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles