Ziyarar Bazata: Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso Ya Ziyarci Asibitin Maikalwa 

Ziyarar Bazata: Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso Ya Ziyarci Asibitin Maikalwa 

Daga Wakilin Mu

A safiyar ranar Talatar nan ne  Shugaban Karamar Hukumar Kumbotso, Comrade Abdullahi Ghali Basaaf, ya kai ziyarar bazata zuwa asibitin Maikalwa domin duba yadda ake gudanar da aiki da kuma Yadda  ma’aikata ke halartar wurin aikin su.

Shugaban ya isa asibitin tun da misalin ƙarfe 8:25 na safe, inda ya zauna har zuwa ƙarfe 9:15 na safe yana jiran ma’aikatan su iso wajen aiki. Sai dai abin takaici, yawancin ma’aikatan ba su bayyana ba, sai jami’in da ke kula da asibitin da kuma ɗaya daga cikin ma’aikatan dindindin kawai aka samu a wurin.

A yayin ziyarar, Comr. Abdullahi Ghali Basaaf ya bayyana cewa, domin karfafa ma’aikata masu nuna jajircewa da gaskiya, ya amince da ɗaukar Malam Garba Mai Gadi da Hajiya Mai Shara a matsayin ma’aikatan wucin gadi na asibitin. Wannan ya biyo bayan kwazonsu da tsantseni wajen aiki, inda aka same su a wurin tun kafin isowarsa.

Shugaban ya bayyana cewa wannan ziyarar bazata tana cikin tsarin tabbatar da ingantaccen kulawa da aiki a karkashin Karamar Hukumar Kumbotso, tare da tabbatar da cewa dukkan ma’aikata suna aiwatar da ayyukansu yadda ya dace.

Ziyarar ta kuma nuna irin jajircewa da shugabanci nagari da Comrade Basaaf ke gudanarwa wajen inganta harkokin lafiya da walwalar al’umma a Kumbotso.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles