26.6 C
Kano
Monday, January 26, 2026

Shugaban Karamar Hukumar Dala Ya Gargadi Yan Kwamitin Raban Taki, Ya Kaddamar da Ayyukan Raya Yan

Shugaban Karamar Hukumar Dala Ya Gargadi Yan Kwamitin Raban Taki, Ya Kaddamar da Ayyukan Raya Yan

Daga Sani Ahmad Sagagi 

Shugaban Karamar Hukumar Dala, Alhaji Surajo Imam, ya kaddamar da wani kwamiti na musamman da zai kula da rarraba takin zamani kan farashi mai sauki, domin sauƙaƙa wa manoma tsadar takin da suke fuskanta.

A yayin taron kaddamar da kwamitin, Alhaji Surajo ya ja hankalin membobin kwamitin kan bukatar su nuna gaskiya da kwarewa wajen gudanar da aikin. An kayyade cewa za a sayar da kowane buhu na takin akan farashin Naira dubu ashirin (₦20,000), wanda hakan ke nuna ragin kashi hamsin cikin dari (50%) ga manoma.

A wani cigaban, Shugaban Karamar Hukumar ya kaddamar da sabuwar makarantar firamare ta Hussaini Adamu da ke Tsamiyar Zubau, wadda aka sanya wa sunan tsohon kansilan mazabar.An gyarar makarantar ta hanyar sake fasalin ajujuwa, tagogi, kofofi, da rufin, inda aka kashe miliyoyin Naira.

Hakazalika, Alhaji Surajo Imam ya bayyana cewa a lokacin mulkinsa, Karamar Hukumar ta samu nasarar gina masallatai sama da goma (10) a wurare daban-daban, gami da gyaran masallacin Juma’a da ke ‘Yan Katako a Rijiyar Lemo da kuma aikin gina titin Daiba.

A ƙarshe, ya bukaci al’ummar yankin su ci gaba da goyon bayan shugabancin Karamar Hukumar domin samun ci gaba da gudanar da ayyukan raya yankin.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles