19.2 C
Kano
Tuesday, January 27, 2026

Kotun Japan ta yanke hukuncin biyan dala miliyan 1.4 ga wani mutum da ya shafe shekaru 44 a gidan yari 

 

Kotun Japan ta yanke hukuncin biyan dala miliyan 1.4 ga wani mutum da ya shafe shekaru 44 a gidan yari

Kotun Japan ta yanke hukuncin biyan dala miliyan 1.4 ga wani mutum da ya shafe shekaru 44 a gidan yari na hukuncin kisa saboda wani kisan da aka yanke masa hukunci amma daga baya aka soke shi, kamfanin watsa labarai na kasar Japan ya bayyana.

Kotun gundumar Shizuoka, wani birni da ke yammacin Tokyo a babban tsibirin Japan, ta umurci gwamnati da ta biya Iwao Hakamada yen miliyan 217 a ranar Litinin. Mista Hakamada, mai shekaru 89, ya shafe shekaru 44 a gidan yari na hukuncin kisa bayan an yanke masa hukunci da laifin kisan mutane hudu a shekarar 1966.

Lauyoyinsa sun yi iƙirarin cewa ‘yan sanda sun tilasta masa ya furta laifin da kuma ƙirƙira shaidu, wanda ya sa aka sake yi masa shari’a a bara kuma aka wanke shi. Ana kyautata zaton shi ne mutum da ya fi dadewa a gidan yari na hukuncin kisa a duniya.

Kudin da aka biya shi, wanda watakila shine mafi girma a tarihin Japan game da shari’ar laifuka, ya kasance diyya ga shekaru sama da 47 da Mista Hakamada ya shafe a gidan yari, kamar yadda kamfanin watsa labarai na Japan, NHK, ya ruwaito.

Kudin yana da kusan dala 83 ga kowace rana da ya shafe a gidan yari.

A cikin shekaru da suka gabata, Mista Hakamada, tsohon ɗan dambe a nauyin featherweight, ya sha bayar da shaida cewa ‘yan sanda ne suka tilasta masa ya amsa laifin bayan sun yi masa tambayoyi na kwanaki 20, suna dukansa da sanda da kuma hana shi barci. Nan da nan bayan ya amsa laifin, ya janye furucinsa.

Kotun Koli ta Japan ta yanke masa hukuncin kisa a shekarar 1980. A shekarar 2014, lauyoyin Mista Hakamada sun sami nasarar sake yi masa shari’a kuma aka sake shi bayan gwaje-gwajen da suka nuna cewa jinin da ‘yan sanda suka yi amfani da shi a matsayin shaida ba ya ɗauke da DNA dinsa.

Bayan Kotun Gundumar Shizuoka ta ba Mista Hakamada damar sake shari’a a shekarar 2014, Kotun Koli ta Tokyo ta soke hukuncin kuma ta ƙi sake buɗe shari’ar. A shekarar 2020, Kotun Koli ta goyi bayan kotun gunduma kuma ta umurci a sake yi masa shari’a, wanda ya ƙare da wanke shi a watan Satumba.

A safiyar ranar Talata, ɗaya daga cikin lauyoyin Mista Hakamada, Hideyo Ogawa, ya shaida wa manema labarai cewa kudin da aka biya shi zai ɗan rama waɗancan wahalhalun da ya fuskanta.

“Ƙasar ta aikata laifi a kansa,” in ji Mista Ogawa.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles