Daga Maikudi Muhammad Marafa

An yabawa Gwamnatin Ganduje bisa inganta fannin lafiya a matakin farko
Mai Bawa Gwamna Shawara a fannin Lafiya a matakin farko Abubakar Usman Kabara ne ya bayyana hakan a wajen taron mika takardar ajiye aiki bisa umarnin da Gwamnan jihar Kano ya bayar ga Masu rike da mukamin daya naɗa.
Hon. Kabara yace, fannin lafiya a matakin farko ya sami bunkasa ta fannin samar da kayan aiki, Karin daukar Ma’aikata da kuma kirkirar sabbin bangarorin kula da aikin ido da sashen kula da hakori da sauran muhimman bangarorin inganta lafiya a matakin farko daban-daban.
Mai Bawa Gwamna Shawara na musamman ɗin daga nan sai ya godewa Babban Gwamna Ganduje bisa damar daya bashi domin bayar da tashi gudunmawar akan harkokin lafiya a matakin farko.
Haka kuma ya godiyawa Babban Sakataren Hukumar Lafiya a Matakin farko Dr. Tijjani Hussaini dama sauran ma’aikatan bisa hadin Kai da goyon bayan da suka bashi domin samun nasarar gudanar da ayyukan sa a ma’aikatar.

