
Kungiyar Matasan Najeriya reshen Karamar Hukumar Shanono ta zabi sababbin shugabanni don gudanar da harkokinta na tsawon shekaru uku masu zuwa.
Wadanda aka zaba sun hada da Auwalu Lawan Sani a matsayin Shugaba, Aliyu Salisu Lawan Mataimakin Shugaba, Abba Usman Ahmed a matsayin Ma’ajin Kudi, da Sirajo Garba a matsayin Jami’in Hulda da Jama’a.
Sauran su ne Anas Hudu Leni Mataimakin Sakatare, Abdulmalik Adam Sakataren Kudi, da Mika’il M Sale Akawu, yayin da Wasila Lawan ta zama Shugabar Mata.
Bayan zaben, sabon shugaban, Auwalu Lawan Sani, ya yi godiya ga dukkan mambobin saboda amincewar da suka yi masa tare da yin alkawarin yin aiki tuƙuru don samun nasara.
Shugaban kungiyar, Alh. Abubakar Barau, wanda Shugaban Sashen Ci Gaban Al’umma, Alh. Gambo Isyaku Gwarzo ya wakilta, ya yi kira ga sababbin shugabannin su kasance jakadu nagari na yankin a kowane lokaci.
Ya kuma ba su shawarar su kasance masu himma wajen kula da walwalan matasa a Shanono.
Hafsat Garba
Jami’ar Yaɗa Labarai Ta Karamar hukumar Shanono

