’Yan Kasuwar Bagwai Sun Nemi Gaggauta Inganta Kayayyakin More Rayuwa a Kasuwar Tumatir ta Marafa
Daga Maikudi Muhammad Marafa
’Yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a Karamar Hukumar Bagwai sun yi kira ga Shugaban Karamar Hukumar da ya gaggauta samar da muhimman kayayyakin more rayuwa a sabuwar Kasuwar Tumatir ta Marafa domin inganta harkokin kasuwanci da walwalar ’yan kasuwa
Kasuwar Yan Tumatir Ta Marafa a Bagwai.
An gabatar da wannan roko ne a yayin wata ganawa da Jami’in Yada Labarai na yankin, Malam Shehu Bello Shanono, ya shirya, wadda ta hada ’yan kasuwa, dillalan tumatir da sauran masu ruwa da tsaki.
Karanta:Karo na Biyu: An Raba Tallafin Kayan Abinci da Kudi na Sama da Naira Miliyan 42 a Kano.
A yayin tattaunawar, mahalarta sun bayyana bukatar gina ingantattun rumfunan kasuwa, samar da tsaftataccen ruwan sha, da kuma gina masallaci a cikin kasuwar. Sun jaddada cewa wadannan kayayyaki na da matukar muhimmanci wajen samar da tsari mai kyau, tsafta da kuma yanayi mai dacewa ga kasuwanci.
Sun kuma nuna cewa rashin wadannan muhimman abubuwa na iya kawo cikas ga bunkasar kasuwar, rage ingancin harkokin kasuwanci, tare da shafar jin dadin masu saye da sayarwa.
Da yake jawabi a yayin taron, Shugaban Dillalan Tumatir, Alhassan Usman, ya bayyana bukatun a matsayin wajibi, tare da kira ga Shugaban Karamar Hukumar da ya dauki matakin gaggawa. Ya kara da cewa samar da rumfuna da tsaftataccen ruwa zai taimaka wajen kare lafiyar ’yan kasuwa da kuma tabbatar da dorewar harkokin kasuwanci.
Haka kuma, Shugaban Kungiyar ’Yan Kasuwar, Ya’u Shafiu Kwajale, ya jaddada muhimmancin gina masallaci a cikin kasuwar domin bai wa ’yan kasuwa damar gudanar da ibadunsu cikin sauki ba tare da tangarda ga harkokinsu ba.
Ya kuma yaba da kokarin gwamnati a wasu fannoni, tare da bayyana fatan cewa za a duba wannan bukata cikin gaggawa.
Dukkanin masu ruwa da tsaki sun bukaci hukumomin Karamar Hukumar Bagwai da su dauki wannan roko da muhimmanci, domin tabbatar da cewa Kasuwar Tumatir ta Marafa ta zama abin koyi wajen tsari, tsafta da ci gaban tattalin arziki.
Sanya hannu:
Jami’in Yada Labarai
Karamar Hukumar Bagwai
Malam Shehu Bello Shanono
