Karo na Biyu: An Raba Tallafin Kayan Abinci da Kudi na Sama da Naira Miliyan 42 a Kano.

Karo na Biyu: An Raba Tallafin Kayan Abinci da Kudi na Sama da Naira Miliyan 42 a Kano.

Daga Sani Ahmad Sagagi

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Yabawa Kwamishinan Ma’aikatar Kasa da Tsare-tsare Bisa Tallafawa Kungiyoyin Al’umma Da ke Jihar Kano.Kayan Abinci Da aka Rabawa Kungiyoyi A Kano

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin Mai ba shi Shawara kan Harkokin Siyasa, Alhaji Hamza Buhari, ya bayyana haka a yayin rabon kayan abinci da Kwamishinan Ma’aikatar Kasa da Tsare-tsare, Abduljabbar Muhammad Umar, ya shirya domin tallafawa kungiyoyin al’umma da ke jihar Kano.

Ya yabawa kokarin Kwamishinan kan ayyukan alkhairi da yake gudanarwa, yana mai jaddada cewa irin wadannan shirye-shirye na taimakawa wajen inganta rayuwar al’umma. Ya kuma tabbatar da cewa zuwa ranar Talata, an raba kayan abinci da kudade da jimillar su ta kai sama da Naira miliyan 42.

A nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Kasa da Tsare-tsare, Abduljabbar Muhammad Umar, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka gudanar da taron na rana ta biyu, inda aka raba kayan abinci da kudade ga kungiyoyin al’umma da na jam’iyya domin tallafa musu.

Taron ya samu halartar Shugaban Jam’iyyar APC na Jiha Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa, tare da wasu Kwamishinoni, masu bai wa Gwamna shawara, shugabannin sassan gwamnati, da kuma masu shirya fina-finan Hausa.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles