Mutane Dubu Uku Sun Amfana da Tallafin Abinci a Kano

Mutane Dubu Uku Sun Amfana da Tallafin Abinci a Kano

Daga Sani Ahmad Sagagi

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya yaba da ƙoƙarin Kwamishinan Ma’aikatar Kasa da Tsare-tsaren Birane ta Jihar Kano, Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar, kan shirin bayar da tallafin kayan abinci ga ƙungiyoyi guda ashirin da takwas, wanda ya anfani kimanin mutane dubu uku a jihar.IMG 20260316 220141

Gwamnan, wanda Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar Kano, Sheikh Tijjani Auwal, ya wakilta a wajen taron rabon tallafin, ya buƙaci waɗanda suka amfana da tallafin da su ma su taimaka wa wasu mabukata da abin da suka samu.

A nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Kasa da Tsare-tsaren Birane, Alhaji Abduljabbar Muhammad Umar, ya bayyana cewa mutane kimanin dubu uku ne suka amfana da tallafin, inda kowannensu ya samu buhun shinkafa guda ɗaya, katan ɗin taliyar spaghetti da kuma tsabar kuɗi Naira dubu ashirin domin taimaka musu wajen kammala azumin watan Ramadan cikin farin ciki tare da shirin bikin Ƙaramar Sallah.

Ya bayyana hakan ne yayin bikin rabon kayan da ya gudana a harabar Gidan Gwamnatin Jihar Kano a yau Litinin. Ya ƙara da cewa an bayar da tallafin ne bisa umarnin Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, wanda ya umarci jami’an gwamnati su ci gaba da sauka ƙasa domin kula da al’umma.

A nasa ɓangaren, Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya buƙaci al’umma da su riƙa ƙara himma wajen gudanar da irin waɗannan ayyukan alkhairi, yana mai jaddada irin girman ladan da Allah ke bayarwa ga masu taimakon mabukata.

Taron ya samu halartar wakilan manyan darikun Musulunci da suka haɗa da wakilin Darikar Kadiriyya, Malam Lasmar Sheikh Nasiru Kabara; wakilin Darikar Tijjaniyya, Malam Hassan Sani Kafinga; da kuma wakilin Kungiyar Izala, Malam Mujahid Aminuddeen.

Haka kuma taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da sauran al’umma daga sassa daban-daban.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles