Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa Ya Amince da Biyan Sama da Naira Miliyan 9 domin Tallafa wa Dalibai
Daga Maikudi Muhammad Marafa
Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Anas Mukhtar Bello Danmaliki, ya amince da fitar da kudade domin biyan wasu muhimman bukatun karatu ga daliban da karamar hukumar ke daukar nauyin karatunsu a manyan makarantu daban-daban.
A karkashin wannan amincewa, an sahalewa biyan jimillar Naira miliyan tara da dubu dari hudu da hamsin da biyu (₦9,452,000) domin tallafawa daliban wajen biyan kudaden karatu da suka hada da kudin rajistar tantancewa (Indexing), kudin rajista da kuma kudin masauki (hostel).
Da farko, shugaban karamar hukumar ya amince da biyan Naira miliyan shida da dubu dari biyu (₦6,200,000) ga dalibai 71, domin biyan kudin rajistar tantancewa (Indexing) dinsu Kwalejin Kimiyya da Fasahar Lafiya ta Jihar Kano da ke Bebeji, tare da Makarantar Kula da Tsaftar Muhalli (School of Hygiene).
Haka kuma, ya amince da biyan Naira miliyan biyu da dubu dari bakwai da hamsin da biyu (₦2,752,000) ga daliban da karamar hukumar ke daukar nauyin karatunsu a Kwalejin Ilimi ta Tarayya ta Fasaha da ke Bichi. domin biyan kudin rajistar NCE II da kudin masauki (Hostel).
Bugu da kari, shugaban karamar hukumar ya sahalewa biyan Naira dubu dari biyar (₦500,000) domin biyan kudin rajistar tantancewa (Indexing) ga dalibai shida (6) da ke karatu a Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasahar Lafiya ta Bichi Academy wadanda su ma karamar hukumar ke daukar nauyin karatunsu.
A Wata Sanarwa da Auwal Ibrahim Galadima Sakataren Tallafin Karatu na Karamar Hukumar Dawakin Tofa ya fitar ya Bayyana cewar Wannan mataki na daga cikin kokarin da shugabancin Karamar Hukumar Dawakin Tofa ke yi na bunkasa ilimi da tallafawa matasa, domin su samu ingantaccen ilimi da kwarewar da za su amfani al’umma.
