Hukumar Kula da Lafiyar Matakin Farko ta Jihar Kano (KSPHCMB) ta gudanar da taron tabbatar da Rahoton Binciken Farko (Baseline Assessment Report) na Shirin Ƙarfafa Tsarin Lafiya na Kano (HSS) a hedikwatarta da ke Naibawa, Kano. Darakta Janar na Hukumar, Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ne ya jagoranci taron tare da haɗin gwiwar Sanitas Health and Development Foundation (SANHDEF), ƙarƙashin jagorancin Shugaban Tawagar Jiha, Saidu Zakari.
A Sanarwa da Jami’ar Yada Labarai Sa’adatu Sulaiman ta Hukumar ta fitar ta Bayyana create An shirya taron ne domin tantancewa da tabbatar da sakamakon rahoton binciken farko na Shirin HSS na Jihar Kano, da kuma samar da fahimtar juna tsakanin masu ruwa da tsaki kan gibin da aka gano da muhimman fannoni da suka fi buƙatar kulawa. Haka kuma, taron ya bai wa masana da masu ruwa da tsaki damar bayar da gudunmawar fasaha domin ƙarfafa shawarwarin ƙarshe na rahoton. Binciken farko ya bayar da cikakken haske bisa hujjoji kan halin da ake ciki na ayyukan kula da lafiya a matakin farko a dukkanin ƙananan hukumomi 44 na jihar, wanda zai zama tubali na gyare-gyaren da za su inganta tsarin da kuma isar da ingantattun ayyukan lafiya.
A nasa jawabin, Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim ya jaddada muhimmancin tsare-tsare masu dogaro da sahihan bayanai da kuma haɗa kan masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da dorewar gyare-gyaren ɓangaren lafiya. Ya kuma sake tabbatar da aniyar Hukumar na rungumar gaskiya da riƙon amana tare da ƙarfafa haɗin gwiwa domin samar da ingantattun ayyukan lafiya masu adalci ga al’ummar Jihar Kano.
Taron tabbatar da rahoton ya haɗa manyan masu ruwa da tsaki da ƙwararrun masana, waɗanda gudunmawarsu za ta taimaka wajen tsara tsari na ƙarshe na aiwatar da Shirin HSS. Hukumar ta sake jaddada ƙudirin ta na mayar da sakamakon da aka tabbatar zuwa tsare-tsaren aiki masu tasiri domin ƙarfafa tsarin kula da lafiyar matakin farko da kuma inganta lafiyar al’umma a faɗin jihar baki ɗaya.
