ME YA SA KO YAUSHE BARAU JIBRIN ? LABARIN CIKIN GIDA NA CIN AMANA NA SIYASAR KANO DA YAƙIN DA AKE WA JAGORA MAI HASKAWA.
Daga Shariff Aminu Ahlan
Idan mutum ya fara haskakawa fiye da yadda abokan hamayyarsa suka zata, kishi da hassada sukan zama makamin marasa ƙarfi. A yau a Kano, iska ta siyasa ta cika da ɓacin rai, dabaru da ƙirƙirar karya, dukkan su kuma suna nufin mutum guda: Sanata Barau I. Jibrin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na Najeriya kuma ɗaya daga cikin manyan jagororin Arewa.
Tambayar da ke yawo cikin fadar iko ita ce mai sauƙi amma mai zurfi: “Me ya sa koyaushe Barau Jibrin?” Tsawon watanni, wata ƙungiyar ‘yan siyasa masu fushi da ba sa da farin ciki, daga cikin jam’iyya da wajen ta, ke shirya yaƙin farfaganda da sharri domin su bata sunan Barau. Duk lokacin da aka samu jinkiri, ko wani abu bai yiwu ba daga Kano, wanda ya shafi samun matsayi a gwanatin tarayya, sai su juya lamarin suce shi ne ya haddasa.
Lokacin da aka jinkirta tabbatar da nadin Injiniya Ramat a matsayin shugaban hukumar Nigerian Electronic Regulations Agency, ‘yan adawa nan da nan suka fitar da ƙarar su ta kullum, “Barau ne ya hana!” Suka zarge shi da tsoron kada a fi shi haske. Wannan ƙarya ce babba, marar tushe.
A matsayinsa na Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau yana jagorantar majalisa bisa bin ka’ida da cancanta ba don kishi ko son zuciya ba. Amma a yanayin siyasar Kano mai guba, gaskiya tana rasa daraja, ana musanya ta da ƙirƙirar labaran sharri. Ya zama ruwan dare: duk wani jan kafa da ya shafi ɗan asalin Kano a Abuja, sai a jingina da Barau. Wadanda ke da kishi sun maida “cin mutunci” sana’a.
Lokacin da aka canza nadin Dr. Maryam Shetty a hukumar North West Development Commission, su ma waɗannan masu neman tashin hankali suka fitar da ihu, “Barau ne ya soke ta!” Babu hujja, babu dalili, sai hayaniya. Suka ƙirƙiro labari suna nuna shi a matsayin wanda ke jan igiyar nadin mukamai a Abuja, alhali gaskiya ɗaya ce: laifinsa shi ne samun tasiri, ci gaba, da karɓuwa daga jama’ar Kano.
Wata cikin mafi ban dariyar zargi ita ce cewa yana amfani da kusancinsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen samun mukamai ga magoya bayansa. Amma me ke da laifi a cikin hakan? A siyasa, tasiri iko ne, kuma iko ana amfani da shi ne wajen samun ci gaba. Barau yana amfani da nasabarsa da gwamnati wajen kawo alheri ga jama’a, ba don cutar da kowa ba.
Ganin yadda ya taka rawa wajen nadin Ministan Jiha, Shugaban North West Development Commission, da kuma Salisu Sagir Takau a matsayin State Coordinator na Renewed Hope Agenda, ya nuna hazakar siyasa da hangen nesa. Duk da haka, bai taɓa tozarta wani ɗan Kano da aka nada a mukami ba, a’a — sau da dama yana nuna farin ciki da alfahari idan ɗan Kano ya samu mukami a matakin ƙasa, ko da kuwa daga jam’iyyar adawa ne.
Barau ya fahimci cewa a tafiyar siyasa, wanda zai tsira dole ya gina tsari mai ƙarfi. Yana gina gada, ba bangon rabuwa ba. Baya ga siyasa, Sanata Barau Jibrin ya samu soyayyar jama’a ta hanyar ayyuka masu gamsarwa. A Kano ta Arewa da ma sauran yankuna, sunansa ya zama alamar ci gaba.
Daga gina manyan hanyoyi, sabunta makarantu, da gina cibiyoyin lafiya, zuwa shirye-shiryen taimakon matasa, Barau ya sake fasalin ma’anar “aiki don jama’a.” Shirinsa na tallafawa ɗalibai, bayar da guraben karatu, da gyaran makarantu, sun canza rayuwar dubban iyalai.
A ƙarƙashinsa, shugabannin jam’iya, matasa da mata sun karɓi motoci, babura, injinan dinki, kayan noman ban ruwa, taki, da jari, domin su fara sana’a, su dogara da kansu. Waɗannan ba alkawura ba ne, su ne hujjojin da ake gani da ido da suka mayar da sunan Barau Jibrin tamkar gida-gida a Kano ta Arewa.
Abin da ya bambanta shi da sauran ‘yan siyasa shi ne daidaito da jajircewa. Tun kafin ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, yana yin ayyukan alheri cikin natsuwa ba tare da neman yabo ko lada ta siyasa ba. Shirinsa na tallafawa jama’a ba ya da alaƙa da zaɓe, jari ne na ci gaban al’umma. Wannan ne ke razana abokan adawarsa: domin aikinsa yana magana fiye da maganganunsu.
Tashin darajarsa a siyasa ya fusata masu yin siyasa da dabaru da hayaniya. Natsuwarsa, basirarsa, da kusancinsa da Shugaban Ƙasa sun mai da shi mabuɗin tasiri a siyasar Kano. Ga waɗanda ke ƙoƙarin rage shi, Barau a 2027 shi ne mafarkin da ba su son ya tabbata.
Yanzu haka, ayyukansa, manyan tituna, shirye-shiryen ilimi, taimakon matasa, sun mai da shi abin koyi a jihar da ke neman jagora nagari. Ba su iya yin gasa ta cancanta, sai suka koma ga ƙarya da farfaganda — dabara ce tsohuwa a siyasa.
A yau, yana bayyana cewa Barau ya zama mutum wanda ba su da ƙarfin fafatawa da shi. Yana mai da hankali ga aikin gwamnati, ci gaban ƙasa, da haɗin kai. Ba ya mayar da martani ga ƙaryarsu, domin shugaba na gaskiya ba ya fafatawa da marasa daraja.
Asalin rikicin kuwa shi ne 2027. Ba batun nadin mukamai ba ne, batun tsoron makoma ce. Waɗanda ba su da abin nunawa sai surutu suna tsoron tasirin Barau a gaba. Sun gane cewa yana da ikon sake fasalin siyasar Kano ta gaskiya da mutunci, shi ya sa suke faɗa da shi da sharri. Amma tarihin siyasa bai taɓa taimakawa masu ƙarya ba, gaskiya tana da ɗorewa.
Barau Jibrin ya zama abin hassada ne saboda yana wakiltar abin da yawancin ‘yan siyasa ke tsoro: ƙwarewa, mutunci, da kusanci da talakawa. Sunansa ya zama alamar natsuwa da hangen nesa, yayin da na abokan hamayyarsa ke wakiltar ruɗani, ƙarya, da rauni.
Yaƙin farfaganda da ake yi masa zai rushe kamar yadda kowace ginin ƙarya take rushewa. Domin Barau Jibrin, hanya ɗaya ce a gabansa, ya ci gaba da yi wa Najeriya hidima cikin tawali’u, jajircewa, da gaskiya.
Jama’ar Kano sun gane gaskiya. Ba da daɗewa ba tambayar ba za ta zama “Me ya sa koyaushe Barau Jibrin?” ba, za ta zama “Wane ne zai iya tsaya wa da Barau Jibrin?”
Shariff Aminu Ahlan Mai Taimaka wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa DSP Barau I. Jibrin ta Bangaren Labarai.
realahlan0101@gmail.com
