Karamar Hukumar Birni da Kewaye Ta Kaddamar da Sabon Injin Wutar Lantarki a Tudun Wuzirci

Karamar Hukumar Birni da Kewaye Ta Kaddamar da Sabon Injin Wutar Lantarki a Tudun Wuzirci

—Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu yabo bisa goyon bayan ayyukan raya kasa

Daga Maikudi Muhammad Marafa

A ci gaba da goyon baya ga manufofin Gwamnatin Jihar Kano wajen inganta rayuwar al’umma, Karamar Hukumar Birni da Kewaye ta kaddamar da aikin saka sabon injin wutar lantarki a unguwar Tudun Wuzirci domin saukaka wahalar da mazauna yankin ke fuskanta na rashin wuta tsawon watanni.

A wata sanarwa da Jami’in Yada Labarai na Karamar Hukumar, Abdullahi Musa Gyadi Gyadi, ya fitar, ya bayyana cewa a yayin taron kaddamarwar, Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo, ya yi kira ga al’umma da su kare kayayyakin da gwamnati ke samarwa don amfaninsu.

Ya ce lokaci ya yi da jama’a za su tashi tsaye wajen kula da duk wani aiki ko kayan more rayuwa da gwamnati ta samar, tare da tabbatar da cewa ba a lalata ko sace su ba.

Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo ya yabawa al’ummar Tudun Wuzirci bisa hakurin da suka nuna a tsawon watanni shida ba tare da samun wutar lantarki ba, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na kokarin shawo kan irin wadannan matsaloli a sauran unguwanni cikin karamar hukumar.

Ya kara da yin godiya ta musamman ga Gwamnatin Jihar Kano a karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, bisa tallafi da goyon bayan da take baiwa Karamar Hukumar wajen aiwatar da ayyukan raya kasa da walwalar al’umma.

A nasa bangaren, Kansilan Mazabar Tudun Wuzirci, Alhaji Aliyu Tukur Sagagi, ya godewa gwamnatin jihar da majalisar karamar hukumar bisa samar da injin wutar lantarkin, yana mai tabbatar da cewa za su kula da injin din tare da tabbatar da ci gaba da amfani da shi yadda ya kamata.

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles