KAROTA  ‘DA YAN SANDA SUN RATTAƁA HANNU DOMIN INGANTA TSARO A JIHAR KANO

KAROTA  ‘DA YAN SANDA SUN RATTAƁA HANNU DOMIN INGANTA TSARO A JIHAR KANO

Daga Maikudi Muhammad Marafa

Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) da Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano sun rattaba hannu kan yarjejeniya ta musamman domin yin aiki kafada da kafada wajen inganta tsaro da tabbatar da doka da oda a fadin Jihar Kano.

A wata Takardar Sanarwa Mai Dauke dasa  hannun Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Abubakar Ibrahim Sharada yace, An cimma wannan matsaya ne yayin ziyarar da Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da Metro Area Command, Ibrahim Abubakar Jauro, ya kai ofishin hukumar KAROTA .

A yayin ziyarar, ACP Ibrahim Abubakar Jauro ya bayyana cewa, rundunar ta fahimci yadda hukumar KAROTA ke gudanar da aikinta cikin tsari da kuma yadda ayyukanta ke da kusanci da na ‘yan sanda, lamarin da ya sa suka ga dacewar yin aiki tare don ƙarin inganci da hadin kai.

Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Hukumar KAROTA, Hon. Faisal Mahmud Kabir, ya bayyana matuƙar farin cikinsa da wannan ci gaban, inda ya ce hakan alama ce ta fahimtar juna da kuma nufin haɗin kai tsakanin hukumomi domin ci gaban jihar.

Ya ƙara da cewa, dukkan nasarorin da hukumar KAROTA ke samu a halin yanzu ba za su yiwu ba sai da gudunmawar Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda ya nuna cikakken goyon baya da ƙarfafa gwiwa ga hukumar a aikinta na yau da kullum.

Hukumar KAROTA ta tabbatar da cewa zata ci gaba da aiki tare da dukkan hukumomin tsaro domin tabbatar da tsari, doka da oda a Jihar Kano.

A karshe Hon.Faisal Mahmud ya karrama mataimakin kwamishinan yan sandan ACP Ibrahim Abubakar Jauro da lambar girmamawa.

 

Related Articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles