AN KAFA KWAMITIN KULA DA KAYAYYAKIN GWAMNATI A DAMBATTA

Daga Tasiu Jimbo Dawanau

AN KAFA KWAMITIN KULA DA KAYAYYAKIN GWAMNATI A DAMBATTA

A wani bangare na kokarin tabbatar da kiyaye dukiyoyin gwamnati da kuma kula da su yadda ya kamata, karamar hukumar Dambatta ta kaddamar da kwamitin kula da kayayyakin gwamnati mai mambobi goma.

An nada Hakimin Dambatta kuma Sarkin Ban Kano, Dr. Mansur Mukhtar a matsayin Shugaban Kwamitin, tare da Alhaji Abba Tukur a matsayin Sakatare.

Yayin bikin kaddamarwar, Shugaban Karamar Hukumar Dambatta, Alhaji Jamilu Abubakar, ya bayyana cewa an dora wa kwamitin nauyin tattara sahihan bayanai kan fitilun solar da ke aiki da wadanda suka lalace, da kuma kula da gyaran wutar lantarki a cikin garuruwa da kauyuka. Haka kuma za su rika ba da shawarwari masu amfani ga karamar hukuma domin ci gaba mai ɗorewa.

Alhaji Jamilu ya ja hankalin ‘yan kwamitin da su tabbatar sun haɗa kai da mutane nagari da ke zaune a muhimman wurare domin sauƙaƙa gudanar da aikinsu.

Ya kuma roƙi al’ummar yankin da su ba da cikakken goyon baya da haɗin kai ga mambobin kwamitin domin cimma nasarorin da ake fata.

A nasa bangaren, Hakimin Dambatta, Sarkin Ban Kano, Dr. Mansur Mukhtar, wanda Alhaji Baba Ado Mukhtar ya wakilta, ya tabbatar da cewa kwamitin ya shirya tsaf domin gudanar da aiki da gaskiya da rikon amana tare da hadin gwiwa da kowa da kowa don samun ci gaba mai dorewa. Ya yi alkawarin cewa za su tabbatar da amincewar da aka nuna musu.

Related Articles

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Stay Connected

0FansLike
0FollowersFollow
0SubscribersSubscribe
- Advertisement -spot_img

Latest Articles